Me ya sa mutane ke ƙin amfani da takunkumi?

Asalin hoton, Getty Images
Da alama da yawan daga cikin 'yan Najeriya na da yakinin cewa cutar korona ba za ta kama su ba, wannan dalili ya sa wasu daga cikinsu na yin biris da amfani da takunkumi.
Likitoci dai sun yi itifakin cewa amfani da takunkumi na taimakawa wajen hana kamuwa ko yada cutar korona, sai dai wasu mutane na cewa yawaita amfani da shi akwai takura.
A makonnin baya a kan shaida a kusan kowacce kusurwa mutane na sanya takunkumi ko kyalen rufe baki da hanci.
Amma da sannu-sannu galibin mutane sun soma watsi da sanya takunkumin, suna mai korafin cewa yana takura musu ko hana su numfashi da kyau.

Wasu mazauna Jihar Legas ma cewa suka yi dogon lokacin da ake dauka sanye da takunkumi na haifar da jiri, ko da yake ra'ayin wasu ya sha bamban.
Mutane da dama da BBC ta tattauna da su sun ce yanzu an kai matsayin da mutane na amfani da takunkumi ne kawai idan sun hangi jami'an tsaro.
Gwamnatin jihar Legas dai ta umarci mazauna jihar sun rinka saka takunkumi idan za su fita domin kare kai daga kamuwa da cutar korona.
Ba a Legas kawai mahukunta suka umarci amfani da takunkumin ba, jihohi irinsu Kano da Kaduna da birnin Tarayya Abuja sun sanar da dokar tilasta sanya takunkumin.
Kwararu a fanin lafiya sun ce, sun fahimci mutane da dama har yanzu ba su gamsu ma akwai korona ba shi yasa wasu ke ganin kamar ana takura musu.

Halin ko-in-kulla
Najeriya na daga cikin kasashen nahiyar Afirka da cutar korona ke yaduwa a cikin gaggawa musamman a arewacin da wasu sassa kudanci kamar Legas mai yawan masu cutar a kasar.
Irin halin ko-in-kulla da rashin daukan matakan kariya da muhimmanci ya sanya hukumomin lafiya ke ganin za a dau tsawon lokacin kafin a iya shawo kan cutar korona a kasashen Afirka.
Yanzu haka akwai jihohin Najeriya da dama da suka sassauta dokar kulle, amma da alama al'umominsu ba su fiye mayarda hankali wajen bin dokokin bai wa juna tazara ba.
Ko da yake wasu jihohin arewacin kasar da ke ganin cutar ta rage karfi ko yaduwarta na sauki sun bada damar cigaba da hada-hada.
Tun bayan bular cutar korona hukumar lafiya ta WHO ta dukufa fadakarwa da bada shawarwari hanyoyin kariya.
Daga cikin irin matakan da ta shawarci a dauka akwai sanya takunkumi inda za a shiga cikin taron jama'a, yawaita wanke hannu da amfani da sinadarin tsaftacce hannu.











