Coronavirus: Yadda za ku hada takunkumi da kanku

A yanzu ana ta shawartar mutane a Ingila da Scotland da Arewacin Ireland su rika sa takunkumi a shaguna da kuma tashoshin ababen hawa domin takaita yaduwar cutar korona.
Yayin da ake shawartar ma'aikatan lafiya su rika amfani da takunkumin likitoci, za ka iya kokarin hada naka takunkumin kaima.
Ga wasu mabanbanta shawarwarinmu wajen matakan da za a bi na hada takunkumi.
In kana amfani da keken dinki ko kuma za ka yi amfani da tsohuwar rigarka ko kuma ta wata hanyar ta daban, hanyar duk daya ce: kaurin yadin da za a yi amfani da shi girman kariyar da zai iya ba ka, kuma tare da yin nunfashi ba tare da damuwa ba.
Wani bincike ya nuna yadin da yafi dadin amfani wajen hada takunkumin shi ne mai santsi ko kuma wanda aka saka da hannu mai dauke da auduga da yawa. Amma duk da haka za ka iya amfani da abin da kake da shi a gidanka wajen hada takunkumin.
Bari mu fara da mai sauki.


Gwamnati na ba da shawarar a rika wanke hannu ko kuma amfani da man goge hannu kafin da kuma bayan sanya takunkumin.
Za kuma ka iya:
- Kiyaye taɓa idanunka da hancinka da kuma bakinka a kowanne lokaci
- Shaguna na amfani da jakar leda har sai an samu damar wanke su
- A rika wanke takunkumin a kai-a kai - za kuma a iya kai shi wanki, ko kuma a wanke shi da abin wanke kaya na yau da kullum
Misalinmu na gaba na amfani da tsohuwar riga ne, an fi son a yi amfani da tufafi mai tauri ko kuma wadanda aka sirka da roba wajen samar da su. Kuma ba tare da ka dinka komai ba.


Ba dole ba ne takunkumin da ake hadawa a gida ya kare wanda ke sanya shi, in ji gwamnati, amma zai iya takaita harba wa wasu cutar idan kana dauke da ita kuma ba ta nuna alama ba.
Idan kana dauke da cutar korona kuma kana nuna alamu - kamar zafin jiki da tari, kamata ya yi ka zauna a gida kada ka fita, kawai ka keɓe kanka a gida.
Kowanne irin takunkumi kake amfani da shi, ka sani ba zai kasance madadin dokar kulle ba. Tsaftace hannu na da amfani kamar dai yadda aka sani a baya - don haka ka rika wanke hannunka da sabulu a kalla na dakika 20 idan ka koma gida.
Misalinmu na gaba na bukatar manne-manne, za su iya zama cikin saƙi ko kuma masu wahala ya danganta da yadda ka ɗauke su - matukar dai za su maƙale a jiki kuma a iya wanke su shikenan.


Akwai wasu hanyoyi masu yawa na hada takunkumi - akwai kuma misalai da yawa a kafafen sada zumunta da kwararru suka yi suka sa, akan ma hada takunkumi da safa.
Ka tuna cewa za ka iya bukatr sama da guda, don ya zama kana da wanda za ka yi amfani da shi lokacin da ka wanke wani.
Bai kamata a sanya wa yara 'yan kasa da shekara biyu takunkumi ba, ko kuma wadanda ba zai dace da su ba yadda ya kamata.
Duka takunkuman da aka nuna ma'aikatan BBC da ke daukar hotunan bidiyo ne suka yi su










