Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙalubale 5 da ke gaban sabon shugaban riƙo na EFCC
- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dakatar da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, 'yan Najeriya da dama na ci gaba da tattauna wannan batu ganin cewa yana da muhimmanci ga ci gaban ƙasar wadda cin hanci ya yi wa katutu.
A ranar Juma'a ne gwamnatin ƙasar ta naɗa Mohammed Umar a matsayin sabon muƙaddashin shugaban hukumar, sai dai masana na ganin cewa akwai ƙalubalen da sabon shugaban zai iya fuskanta bayan kama aiki, kuma idan ya shawo kan waɗannan kalubalen, da alamu zai iya samun nasara.
BBC ta tattauna da Kabiru Dakata, wanda shi ne babban daraktan cibiyar wayar da kan al'umma kan shugabanci na gari da kuma tabbatar da adalci, Malam Kabiru ya shaida wa BBC ƙalubale biyar da ke gaban wannan sabon shugaba na riƙo:
Dawo da martabar hukumar EFCC
Kabiru Dakata ya bayyana cewa abu na farko da Mohammed Umar ya kamata ya fara yi shi ne dawo da martabar hukumar EFCC a idanun al'umma.
"Sabon shugaban ya zo ne a daidai lokacin da ake tunanin cewa kwarjinin EFCC ya ragu, kuma ba ta ba mutane tsoro kamar baya, kuma a baya ta kasance tamkar inji na yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, sai dai yanzu ana kallonta tamkar ita ce cibiyar cin hanci da rashawa," a cewarsa.
Ya ce ya kamata ya dawo da martabar wannan hukuma ta yadda jama'ar ƙasar za su ci gaba da kallon wannan hukuma da karsashi da kuma dawowa da ita kan asalin doron da aka kafa ta na yaƙi da cin hanci da rashawa.
Guje wa mummunan ƙarshe irin na sauran shugabannin EFCC
Sabon shugaban riƙo na wannan hukuma ya karɓi wannan muƙami a daidai lokacin da ake ganin cewa duka waɗanda suka shugabanci wannan hukuma ba a yi rabuwar lafiya da su ba.
Tun daga kan Nuhu Ribaɗu zuwa Farida Waziri da Ibrahim Lamorde da kuma yanzu Ibrahim Magu, dukansu an zarge su da cin hanci da rashawa.
A cewar Kabiru, ya kamata sabon shugaban ya yi ƙoƙarin ganin cewa "ya gama da wannan aiki lafiya ba tare da wani zargi ba".
Ya bayyana cewa ko da kuwa aiki na mako guda zai yi a EFCC, "ya yi ƙoƙari ya tafi ana Allah san barka ba wai ya bi sahun waɗanda suka gabace shi ba".
Sauya tunanin 'yan Najeriya kan yanayin aikin EFCC
Tun bayan kafa hukumar EFCC a zamanin mulkin Shugaba Obasanjo, jama'a da dama na da ra'ayin cewa an kafa wannan hukuma ne domin yaƙi da masu adawa da gwamnati ko kuma cin zarafin waɗanda ba sa ɗasawa da gwamnati mai ci.
Ƙalubalen da ke kansa shi ne "ya za a yi ya sauya tunanin 'yan Najeriya daga kan wannan tunani ya ɗora su kan tunanin hukumar EFCC za ta yaƙi duk wani salon cin hanci da rashawa, kuma ko wane ne ake zargi da hakan", in ji Kabiru.
Yaƙar cin hanci a baya da na gaba
Cin hanci da rashawa a Najeriya lamari ne da aka daɗe ana yaƙi da shi tun a zamanin jamhuriyya ta farko.
Duk da yaƙin da ake yi da shi, hakan bai sa an fasa cin rashawa ba, kuma ana zargin cewa cin rashawar ce take mayar da hannun agogo baya musamman wurin ci gaban Najeriya ta fannin siyasa da tattalin arziƙi da kuma mulki.
A cewar Kabiru Dakata, "Abin da muke sa rai mu gani shi ne ya za a yi a yaƙi cin hancin da aka yi a baya, ya kuma mayar da hankali kan cin hanci da ake yi a yanzu a gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu, da kuma ɗaiɗaikun jama'a".
Ɗinke ɓarakar da ke cikin EFCC
Kamar yadda ake samun ɓaraka a sauran ma'aikatun gwamnati da hukumomi a Najeriya, da alama a hukumar EFCC ma an samu shigen irin wannan ɓarakar.
Domin a cewar Kabiru Dakata, "an samu ɓaraka a EFCC, domin akwai waɗanda ake kira Magu boys, akwai kamar 'yan bora da kuma 'yan mowa, saboda haka ya za a yi ya ɗinke ɓarakar da ke cikin ma'aikatansu ya haɗa kansu"?
Malam Kabiru ya shaida mana cewa ya san duk irin waɗannan abubuwa ta hanyar aiki da suke yi na ƙungiya da kuma bayanan sirri da suke samu kan irin waɗannan lamura.
Ya bayar da shawarar cewa ya kamata sabon shugaban hukumar na riƙo ya haɗa kan ma'aikatan hukumar domin shi ma ya samu nasara a aikin da zai sa a gaba.