Ibrahim Magu: 'Mun dakatar da shugaban EFCC ne kan manyan zarge-zarge da saɓanin alƙaluma'

Gwamnatin Najeriya ta ce ta dakatar da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, kan wasu manyan zarge-zarge da kuma saɓanin alƙaluma cikin harkokin hukumar.

Ta ce daga cikinsu, dakataccen shugaban ya yi iƙirarin ƙwato kuɗi kimanin dalar Amurka biliyan arba'in da shida amma sai aka taras da biliyan talatin da bakwai a banki. "To, ina biliyan takwas".

Yayin zantawa ta wayar tarho a cikin shirin Ra'ayin Riga na BBC Hausa, mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana "kamar yadda na ce zargi ne, mai yiwuwa ko iya lissafin ne ba a yi ba".

Ya kuma ce hukumar ta ƙwace gidaje 836, amma sai ka ce Ibrahim Magu ya yi tattara alƙluma kuma shigarwa da gwamnati bayanin gida 339. "Ina sauran," in ji mataimakin shugaban ƙasar na musamman.

"Sai kuma aka sake lissafi ka ce a'a 504 ne yanzu gidajen. Duk da haka dai ina ragowar ɗaruruwan gidajen?" Garba Shehu ya tambaya.

Ya ce irin waɗannan batutuwa ne suka janyo gudanar bincike kuma mai yiwuwa Ibrahim Magu na da irin nasa bayanai da zai iya gamsar da su.

Sai dai Malam Garba ya tunasar da cewa duk waɗannan batutuwa har yanzu zargi ne kawai, sai fa idan kwamitin da ke gudanar da bincike ya kammala aiki don tabbatarwa ko akasta su.

Ya ƙara da cewa mai yiwuwa abubuwan nan rashin gaskiya ne mai yiwuwa kuma rashin iya lissafi ne.

Wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a, gwamnati ta ce an dakatar da Ibrahim Magu ne, don kwamitin shugaban ƙasa ya gudanar da bincike kansa ba tare da wani shamaki ba.

Ta kuma ce ta tabbatar da Mohammed Umar a matsayin sabon mukaddashin shugaban EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa.

A cewar Garba Shehu, Ibrahim Magu yana hannun hedikwatar 'yan sandan Najeriya, don ya kasance yana kusa da masu bincike ta yadda zai iya kare kansa.

Haka zalika, ya ce daga cikin zarge-zargen da ake yi wa Magu, akwai batun rashin ba da haɗin kai ga masu bincike na gwamnati dangane da ayyukan hukumarsa.

Hukumar tsaron sirri ta DSS ta yi wani bincike a shekara ta 2019 a kan dakataccen shugaban hukumar EFCC, in ji Garba Shehu.

Ya kuma ce ban da wannan akwai wani kwamiti da gwamnati ta kafa game da kadarorin da EFCC ta ƙwato, amma da ya gama bincike ya shaida wa gwamnati cewa bai samu haɗin kai daga wajen Magu ba.

Karin labarai kan Magu: