Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Ghana: Ghana ta yi atamfar korona
Wani kamfanin yin atamfofi na Ghana ya ƙaddamar da sabbin samfuri na atamfofi da ke nuna irin matakai da kuma halin da aka shiga lokacin annobar cutar korona.
Sabbin atamfofin na da alamomi kamar ƙwado da mukullai da jirgin sama, waɗanda duka matakai ne da aka ɗauka na daƙile yaɗuwar cutar.
Ana yawan saka atamfofi na Afrika a Ghana, kuma ma'aikata da dama na saka su a ranar Juma'a.
An saka dokar kulle a manyan biranen ƙasar biyu a watan Afrilu - kuma a faɗin ƙasar, an saka dokar hana taruwar jama'a da kuma kulle iyakoki.
An sassauta dokar kulle da daɗewa- duk da cewa akwai dokar bayar da tazara musamman a coci-coci - kuma rashin saka takunkumi a bainar jama'a babban laifi ne a ƙasar.
Ƙasar da ke yammacin Afrika ta bayar da rahoton sama da mutum 20,000 da suka kamu da cutar korona inda kuma a kalla mutum 129 suka mutu daga cutar.
"Mu 'yan kasuwa ne da ke bayar da labarin kanmu ta hanyar samfarin atamfofinmu," In ji Mista Badu, wanda shi ne manajan darakta na kasuwanci na kamfanin buga atamfofi na Ghana wato Ghana Textiles Printing.
"Muna da yaƙinin cewa hakan zai shiga cikin tarihi a duniya, kuma yana da kyau waɗanda za a haifa a nan gaba su san da cewa wani abu irin haka ya taɓa faruwa."
Wasu daga cikin samfarin atamfofin da aka buga na da hoton gilas a kan su - wanda gilas din na kama da wanda shugaban ƙasar Nana Akufo-Addo ke sakawa idan yana bayar da bayanai kan korona.
"Yana da wasu gilas da yake sakawa idan kuna kallonsa a talabijin, wannan shi ne yake nufi," in ji Mista Badu.
"Wani samfarin atamfar kuma na nuni da jirgin sama, hakan na nuna cewa ɗaya daga cikin matakan da Ghana ta ɗauka lokacin dokar kulle akwai rufe iyakoki, babu tashin jirage," in ji shi.
A 2004, gwamnatin ƙasar ta fara kiraye-kiraye kan mutane su fara saka tufafi na ƙasa a ranar Juma'a domin tallafa wa masana'antun yin tufafi na ƙasar, sai dai akasarin tufafin da 'yan ƙasar ke sakawa a ranar Juma'a ba kamfanonin ƙasar ke yin su ba.
Kamfanin Ghana Textile Printing duk da sunansa, mallakar kamfanin Vlisco ne na Holland.
Sai dai Mista Badu ya ce sabbin samfarin atamfofin na batu ne kan 'yan Ghana inda suke bayar da labarin kansu.
"Samfarin da muke bugawa a yanzu dukansu daga Ghana aka ƙirƙire su kuma a Ghana ake buga su, duk wani samfari da muka yi, akwa wani amfani garemu." in ji shi.