Coronavirus a Ghana: Sarauniyar Ingila ta karrama dan Ghana kan tallafin Covid 19

Wani dan kasar Ghana da aka yi Yakin Duniya na Biyu da shi Private Joseph Hammond ya ce ya matukar jin dadi da farin ciki bayan samun labarin cewa Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta jinjina wa kokarinsa na tara tallafin kudi a yakin da ake yi da annobar Covid-19.

An karrama shi da lambar yabo ta Commonwealth Points of Light wacce ake bai wa masu aikin sa kai da ke wani abun bajinta a kasashen rainon Ingila.

Mista Hammond wanda ke da shekara 95 a yanzu, ya shiga rundunar Royal West African Frontier ne tun yana dan shekara 16.

A watan da ya gabata ne ya sanya wa kansa yin tafiyar kilomita 3.2 a kowace rana don tara kudi dala 600,000 don sayen kayayyakin kariya ga ma'aikatan lafiya da tallafa wa tsofafin sojoji da ba su da gata.

Zuwa yanzu Private Hammond ya hada dala 35,000.

Ya fara wannan aiki ne don bin sahun wani tsohon soja a Burtaniya Kyaftim Sir Tom Moore, wanda ya tara fiye da dala miliyan 35 ga Hukumar Lafiya Ta Burtaniya.

Jikan Sarauniyar, Yarima Prince Harry, ya rubuta wasikar karfafa gwiwa ga Private Hammond yana mai ba shi goyon baya a farkon watan nan.