Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mai yi wa Sarauniya Elizabeth kwalliya ta fallasa sirrin sarauniya
An fallasa sirrin Sarauniya Ezabel II, a wani sabon littafin da daya daga cikin mutanen da suka fi kusanci da ita ta wallafa.
Angela Kelly ta rubuta littafin wanda ya yi bayani a kan abubuwan da suka faru na sirri, a tsawon shekarun da ta yi tana taimaka wa sarauniyar Ingila wajen sanya kayanta, haka kuma a matsayinta na kawarta.
Hasali dai abin da aka saba gani shi ne, Sarauniya da mai yi mata dinki da kuma tufafin da za ta sanya duka masarauta ce ke amincewa da su.
Dan takaitaccen bayani a kan littafin ya ce "Sarauniyar da kanta ta amince wa Angela ta bayyana wa duniya irin shakuwar da suka yi".
Mujallar Hello ta fara wallafa wasu daga cikin abubuwan da suka ja hankali da littafin ya kunsa.
1. Sai wata ta gwada sabon takalmanin sarauniya
A cikin littafin, Ms Kelly, wadda ke yi wa sarauniya kwalliya tun daga shekarar 2002, ta tabbatar da cewa sarauniyar na da wadda ke taimaka mata wajen gwada sabon takalminta ko zai yi daidai. Kuma mai taimaka mata wajen kwalliyar ce ke yin hakan.
Ms Kelly ta rubuta cewa: "Sarauniya ba ta da lokaci sosai don haka ba ta gwada sabon takalminta, kuma da yake kafarmu daya, sai faduwa ta zo daidai da zama. "
2. Sarauniya ce ta bukaci ta yi magana a wasan James Bond a lokacin bikin bude gasar Olympics a London a shekarar 2012
Ms Kelly ta ce cikin kankanin lokaci "mintoci biyar" da yi wa sarauniya tayin fitowa tare da tauraron fim din James Bond, Daniel Craig ta amince da hakan.
"Batun ya nishadartar da ita sosai, abin da yasa nan da nan ta amince. Sai na tambaye ta ko za ta so ta yi magana? Bata ko musa ba, sai ta amsa da cewa: ' Ai dole na ce wani abu, domin zai zo ceto na ne," A cewar Ms Kelly.
"Na tambaye ta ko za ta so ta ce: 'Barka da maraice, James,' ko kuma: ' Barka da yamma, Mr Bond,' to sai ta zabi na biyun saboda fina-finan Bond din da ta sani. Kafin ka ce wani abu na sanar da labarin ga daraka [Danny Boyle] - Ina ganin sai da ya ji kamar zai fado daga kujerar da yake zaune, saboda na gaya masa cewa sarauniya zata fadi: ' Barka da yamma Mr. Bond.
3. Zuwan sarauniya filin gasar tseren dawaki na Royal Ascot
Mutane kan zuba ido su sha kallon irin dawakin gidan sarauta da sarauniya ke zuwa da su wajen gasar tseren dawaki na Royal Ascot da ake yi duk shekara.
Sai dai ba kawai dawakan mutane ke kallo ba - ta kai har sun zuba kudaden caca kan launin hular da sarauniyar ta sanya.
Ms Kelly ta rubuta cewa: " Na yi wata ganawa da mai shirya cacar, inda muka amince kan lokacin da za a rufe don kada a cuci wasu, amma muka bar mutane suka ci gaba da cankar launin hulal sarauniya domin wanda zai lashe gasar ya samu wasu 'yan kudade."
4. Rungumar Michelle Obama
Rahotanni sun ce sarauniya ta yi "watsi " da al'adar masarauta da ta rungumi matar tsohon shugaban Amurka, Michelle Obama, a lokacin da suka gaisa a shekarar 2009, batun ba haka ya ke ba a cewar, Ms Kelly.
"A zahiri, dabi'a ce ga sarauniya ta girmama macen da ake ganin girmanta, haka kuma babu wata al'adar da ta zama dole a bi. " kamar yadda ta rubuta.
Mrs Obama ta yi rubutu kan abubuwan da suka faru a rayuwarta cewa, su biyun sun amince su sanya takalma masu tsini kuma hakan ya sanya kafafuwansu sun yi tsami.
Mun kasance "mata biyu da takalmanmu suka wahalar da mu",
5. Akwai wani sirrin da ba a sani ba, game da rigar sarauta ta radin suna
Ms Kelly ta bayyana yadda aka yi amfani da "ganyen shayi wajen yin irin rigar da aka taba amfani da ita a radin sunan James, Viscount Severn, a shekarar 2008.
"Don tabbatar da cewa ya yi kama da wancan, an rina rigar a ruwan ganyen shayin da ake shukawa a Yorkshire," Ms Kelly ta rubuta hakan a littafin.
"Mun saka kowane yadin leshin a wani karamin mazubi, muka cika shi da ruwa aka kuma saka ganyen shayin ya tsumu kamar tsawon mintoci biyar, aka ringa dubawa a kai a kai har sai da launin ya yi daidai."