Coronavirus a Kenya: Ba za a koma makaranta a Kenya ba sai 2021

kenya schools

Ma'aikatar Ilimi ta Kenya ta ce ba za a sake bude makarantun firaimari da sakandire ba sai a shekarar 2021.

Ma'aikatar Ilimin ta ce duka daliban za su koma ajujuwan da suke ne a lokacin da aka tafi hutu.

Ministan ilimi George Magoha ya ce babu jarrabawar karshe ga dalibai firaimari da sakandire.

Ana dai yin wadannan jarrabawar ne a watannin Oktoba da Nuwamba na ko wacce shekara.

Amma ya ce Kwaleji da jami'o'i su shirya domin sake budewa a watan Satumbar wannan shekaar amma da wasu sharuda, kuma ya ce wadanda suka cika sharudan ne kawai za a bari su bude.

An rufe makarantu a Kenya ne a watan Maris bayan kasar ta samu mai dauke da korona na farko.