Coronavirus a Afirka: Yaya saurin yaɗuwar cutar a nahiyar yake?

Woman at market in Lagos state, Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya na cikin kasashen da suka fi fama da cutar korona
    • Marubuci, Daga Peter Mwai da Christopher Giles
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check

Ana samun yawaitar masu kamuwa da cutar korona a Afirka sannan kuma masu mutuwa sakamakon cutar suna karuwa, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Mun yi nazari kan halin da ake ciki a nahiyar, da kuma duba kasashen da suka fi fama da ita.

Yaya girman yaduwar cutar korona a nahiyar?

Idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi, har yanzu masu kamuwa da cutar korona a Afirka ba su fi cikin cokali ba, amma saurin yaduwar cutar a wasu kasashen nahiyar abu ne mai tayar da hankali.

Ko da yake sai da aka kwashe kusan kwana 100 kafin a samu mutum 100,000 da suka kamu da cutar korona a Afirka, amma cikin kwana 18 wannan adadi ya ninka zuwa 200,000. Kazalika cikin kwana 20 ya sake nunkawa zuwa 400,000.

Wannan yaduwa da cutar ta korona take yi kamar wutar daji a Afirka ya yi kama da abin da ya faru a wasu yankunan duniya da cutar ta fi yi wa barna. Galibin kasashen Afirka yanzu suna fama da matsalar mutum daya, wanda bai yi mu'amala da wanda ya dauko cutar daga kasar waje ba ko kuma wanda hukuma ta tabbatar yana dauke da cutar ba, ya yadawa mutane da dama a cikin al'umma, a cewar WHO.

Hakan na da hatsari domin kuwa zai bai wa hukumomin lafiya wahalar gano inda ya dauko cutar.

A ina cutar korona ta fi katutu a Afirka?

Kasashen da cutar korona ta fi yi wa katutu a Afirka su ne Afirka ta Kudu da Masar. Suna da fiye da kashi 60 na dukkan mutanen da suka kamu da cutar korona a nahiyar a watan Yuni.

Afirka ta Kudu ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar, yayin da Masar ta fi yawan masu mutuwa sanadin cutar.

Afirka ta Kudu, wacce ta sanya daya daga cikin dokokin kulle mafiya tsauri a duniya a waran Maris, ta fuskanci karuwa sosai ta samu kamuwa da cutar bayan ta sassauta dokar a watan Mayu.

A lardin Yammacin Cape (inda Cape Town yake), a nan aka samu kusan rabin mutanen da suka kamu da cutar a kasar da kuma fiye da rabin mutanen da cutar ta kashe. Amma masu kamuwa da cutar na yawaita a lardin Gauteng, inda birnin Johannesburg yake.

Ana samu karuwar masu kamuwa da cutar a Masar tun daga tsakiyar watan Mayu, kuka akwai alama cutar ta kai kololuwa ganin cewa yanayin kamuwa da ita a kowacce rana kusan iri daya ne tun daga farkon watan Yuli.

Kazalika ana nuna matukar damuwa kan Najeriya, wacce ta zo ta biyu kan karuwar wadanda suka mutu ranar 1 ga watan Yuli bayan Afirka ta Kudu, kamar yadda WHO ta ce.

Short presentational grey line

Kazalika an samu karuwar masu kamuwa da cutar korona a Mauritania, inda kasar ta kasance cikin kasashen da aka fi kamuwa da cutar a makonnin baya bayan nan.

Yana da muhimmanci a sani cewa akwai kasashen da ba a samu wadanda suka kamu da cutar korona da yawa ba, musamman a Gabashin Afirka.

Hasalima, rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniya reshen Afirka ta fitar ya ce kasashe 10 ne suke da kashi 80 na masu dauke da cutar korona a nahiyar.

Mutum nawa ne suke mutuwa a Afirka?

Mutanen da suka mutu a nahiyar sanadin cutar ba su da yawa idan aka kwatanta da sauran nahiyoyin duniya, duk da yake galibin kasshen Afirka ba su da ingantattun hanyoyin kiwon lafiya.

WHO ta ce mai yiwuwa hakan na faruwa ne saboda akasarin mazauna Afirka mataa ne - fiye da kashi 60 na al'ummar nahiyar 'yan kasa da shekara 25. Bincike ya nuna cewa matasa ba su mutu sosai ba sanadin cutar korona.

Sai dai duk da haka akwai kasashen da ake mutuwa sanadin cutar daidai da ko fiye da kason galibin kasashen da ska fi fama da cutar, wato kashi biyar cikin dari:

  • Chadi (8.5%)
  • Algeria (6.6%)
  • Jamhuriyar Nijar (6.2%)
  • Burkina Faso (5.5%)
  • Mali (5.3)

Githinji Gitahi, shugaban Amref Health Africa, wata kungiya da ke kware a kan harkokin kiwon lafiya, ya ce samu karuwar masu dauke da cutar alama ce da ke nuna cewa tana yaduwa sosai fiye da yadda ake sanarwa, ko da yake akan zai iya kasance saboda ba a yin gwaji sosai.

Yaya girman gwajin cutar korona a Afirka?

Kasashe goma su ne ke da kashi 80 na gwajin da ake yi a nahiyar - Afirka ta Kudu, Morocco, Ghana, Masar, Ethiopia, Uganda, Mauritius, Kenya, Najeriya da kuma Rwanda.

Akwaibambanci kan yadda kowacce kasa take gwaji, inda Afirka ta Kudu take yin gwaji sosai, yayin da Najeriya ba ta yin gwaji da yawa, a cewar akaluman da Our World in Data, wata kungiya da ke da mazauni a Birtaniya da ke tattara bayanai kan Covid-19 ta fitar.

Ranar 4 ga watan Yuni, Afirka ta Kudu na gwada mutum 30 cikin mutum 1,000, idan aka kwatanta mutum 72 a Birtaniya da mutum 105 a Amurka.

Najeriya kuwa tana yin gwaji 0.7 kan dukkan mutum 1,000, yayin da Ghana ke gwada mutum 10 inda ita kuma Kenya take gwada mutum 3.

Yana da muhimmanci a sani cewa a wasu kasashen Afirka, zai yi wahala a san takamaiman adadin mutanen da ke kamuwa da cutar saboda rashin isassun kayan aiki.

A Tanzania, Shugaba John Magufuli ya bayyana shakku kan ingancin gwajin da babban dakin gwajin kasar yake yi, kuma ba ya bari a fitar da ainihin bayanai kan girman yaduwar cutar a kasar.

Equatorial Guinea ta fada rikici da WHO bayan ta zargi wakiliyar Hukumar Lafiya ta Duniyar da kara gishiri na adadin masu dauke da cutar.

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, an samu karin mace-mace na mutum kusan 1,000 a watan Afrilu, amma gwamnatin jihar ta musanta cewa galibinsu na da alaka da cutar korona.

Reality Check branding
Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Asalin hoton, NCDC