Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ibrahim Magu: Fadar shugaban Najeriya ta dakatar da shugaban EFCC
Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta Najeriya EFCC.
Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata.
A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba.
Kwamitin - karkashin jagorancin tsohon mai shari'a Ayo Salami - ya gayyaci Mr Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC.
Wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami'an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin.
A ranar ta Litinin ne rahotanni suka nuna cewa jami'an tsaron DSS a kasar sun kama Ibrahim Magu.
Sai dai wata sanarwa da DSS da kuma EFCC suka fitar daban-daban sun ce ba kama Mr Magu ta yi ba.
EFCC ta ce ya amsa gayyatar jami'an tsaro ne kawai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.
Shi ma kakakin DSS Peter Afunanya ya ce: "DSS tana so ta shaida wa al'umma cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban EFCC ba, kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahoto."
Tun da aka bayar da labarin kama shi har yanzu wannan lokaci ba a ga Mr Magu ba.
Rashin fitowar mahukunta a Najeriya su fadi takamammen inda yake, ya ba da kafa ga wasu `yan Najeriya ta yin shaci-fadi ko rade-radi game da al'amarinsa.
Bayanan da ke fitowa na baya-bayan nan dai sun tabbatar wa BBC cewa Mr Magu ya kwana ne a hannun jami'an 'yan sanda masu gudanar da bincike, bayan ya kwashe sa'o'i yana amsa tambayoyi daga `yan kwamitin shugaban kasa, wadanda aka ce za su ci gaba da yi masa kwakwa yau din nan.