Bincike kan Magu: Abubuwan da muka sani kawo yanzu

Lokacin karatu: Minti 2

Binciken da ke yi wa mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Ibrahim Magu, shi ne batun da ya kankane jaridu da shafukan sada zumunta a Najeriya.

Ganin cewa shi ne kan gaba wajen yaki da rashawa a Najeriya, abin ya zo wa 'yan Najeriya da mamaki da aka samu rahotannin cewa shi kansa ana bincikensa bisa zargin cin hanci abin da kuma ya musanta.

Ranar Litinin rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron DSS a kasar sun kama Ibrahim Magu domin yi masa tambayoyi.

Sai dai wata sanarwa da DSS da kuma EFCC suka fitar daban-dabn sun ce ba kama Mr Magu ta yi ba.

EFCC ta ce ya amsa gayyatar jami'an tsaro ne kawai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Ga wasu bayanai da muka samu kawo yanzu kan batun binciken na Magu:

  • Tsohon shugaban kotun daukaka kara a Najeriya, Mai Shari'a Ayo Salami ne ke shugabantar kwamitin bincike kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban EFCC na riko, Ibrahim Magu.
  • Galibin kafafen yada labarai a Najeriya sun wallafa cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami'an tsaro saboda ba'a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin.
  • Ana gudanar da binciken ne a kusa da fadar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja.
  • Hukumar DSS ta ce ba kama shi ta yi ba, amma ta gayyace shi domin amsa wasu tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.
  • EFCC a cikin wata sanarwa ta ce Ibrahim Magu da kansa ya amsa gayyatar kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin binciken kuma ba tursasa masa aka yi ba.
  • Bayanai sun ce binciken na da nasaba da wata wasika da ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya aike wa shugaba Buhari kan zargin shugaban na EFCC na amfani da ofishins ba bisa ka'ida ba.
  • Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, PDP ta bukaci Ibrahim Magu ya sauka daga kujerarsa har sai na kammala bincike.
  • An hana 'yan jarida shiga zauren da ake binciken Ibrahim Magu.
  • Tun a shekara ta 2015 yake rikon kujerar amma ba a tabbatar da shi ba saboda majalisar dattijan Najeriya ta ce hukumar tsaro ta DSS ta aike mata wasu bayanai na rashin gamsuwa kan Ibrahim Magu.

Karin labarai da za ku so ku karanta kan Mr Magu: