Donald Trump: Shugaban Amurka ya yi wa Somalia mummunar fahimta

Asalin hoton, Getty Images
A cikin wasiƙun da 'yan jarida ke turo wa BBC, Ismail Einashe ya yi nazari game da yadda ƙasar Somalia ta shiga cikin yaƙin neman zaɓen Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump na neman mayar da 'yar siyasar nan ta Amurka kuma 'yar asalin Somalia wato Ilhan Omar macen da ya fi caccaka yayin yaƙin neman zaɓensa - hakan ya sa ya haɗa da ƙasarta ta asali wato Somaliya.
A caccakar da ya yi mata na 'yan kwanakin nan a wani yaƙin neman zaɓe a Tusla, Oklahoma, ya zargi Ilhan mai shekaru 37 da neman kawo "fitinar" da ke a Somaliya zuwa Amurka.
"Tana so ta mayar da gwamnatin Amurka irin gwamnatin kasar da ta fito - Somaliya. Ba gwamnati, ba tsaro, ba 'yan sanda, ba komai sai fitina. Sai kuma yanzu tana so ta faɗa mana yadda za mu gudanar da ƙasarmu. A'a mun gode," in ji Trump.
Ms Ilhan ta je Amurka ne tun tana ƙaramar yarinya a 1995, a halin yanzu 'yar majalisa ce mai wakiltar Minnesota, wanda a ƙarƙashinta ne garin Minneapolis yake inda a nan ne aka kashe baƙar fatan nan George Floyd a watan Mayu, abin da ya jawo zanga-zanga a faɗin duniya kan muhimmancin rayuwar baƙar fata.

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai abin da Shugaba Trump ya fi mayar da hankali a kai da ya je Tusla shi ne asalin Ilhan, da alamu domin ya karkatar da hankalin mutane daga rikicin da ke faruwa kusa da gida.
A martanin da Ms Omar ta mayar, ta ce kalaman Trump na "wariyar launin fata" ne. Ta ce fushinsa ya samo asali ne bayan wata ƙuri'ar jin ra'ayinn jama'a ta da ta nuna cewa abokin takararsa na jam'iyyar Democrat Joe Biden yana gaba da shi a jiharta, wanda wuri ne ga 'yan Somalia da dama a Amurka.
Trump ya yi zargin cewa Ms Omar tana cike da "Baƙin ciki da kuma ra'ayin gurguzu," inda ya yi gargaɗin cewa idan abokin takararsa Joe biden ya samu nasara a zaɓe, za ta taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da gwamnatin Amurka.
Hakan na faruwa ne kuwa duk da cewa Ms Omar ba wani shiri take yi da Biden ba, domin kuwa Ms Omar ɗin ta goyi bayan Bernie Sanders ne a baya lokacin zaɓen fitar da gwani.
Tsohon dan jam'iyyar Republican da ke mulkin Somalia
Da alamu yadda Mista Trump ke kallon Somalia ya samo asali ne bayan hamɓarar da gwamnatin Siad Barre a 1991, wanda a lokacin jama'ar duniya ke kallon ƙasar a matsayin wadda ta fi gazawa.
Wannan kallon da ake yi wa ƙasar na nan duk da cewa abubuwa sun sauya a ƙasar.
A lokacin da Mista Trump ke tunanin cewa babu doka da 'yan sanda ko gwamnati a Somalia, wannan ya wuce abin da ke da akwai a zahiri a ƙasa.
Gwamnatin ƙasar da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya na ɗaukar matakai kaɗan-kaɗan na ƙara gina ƙasar da kuma daƙile masu iƙirarin jihadi - da taimakon wasu 'yan Somalia da ke zama a ƙasashen waje da ke dawowa gida.

Asalin hoton, AFP
Ciki har da Shugaban ƙasar na yanzu Mohammed Abdullahi Mohammed wanda aka fi sani da "Farmajo", wanda ɗan jam'iyyar Republican ne mai rajista a Buffalo da ke Amurka, kuma ya bar ƙasarsa ta Amurka inda ya koma Somalia domin ya jagoranci ƙasar a 2017.
Sai dai duk da haka abin da ya faru a 1993 ne ya sa Mista Trump da magoya bayansa ke kallon Somalia a haka - wanda a wannan shekarar ne dakarun Amurka suka kutsa Mogadishu babban birnin ƙasar domin kama jagoran rikicin.

An harbo jirage masu saukar ungulu biyu na Amurka, taro da kashe sojojin Amurka 18, sama da 'yan Somalia 500 ne aka kashe yayin yaƙin.
Abin da ya faru da sojojin ya jawo ce-ce-ku-ce a Amurka wanda hakan ya yi illa kan dangantakar Amurka da ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Musulma mai son saka Hijabi
Wargajewar Somalia kusan shekaru 30 da suka wuce ya sa 'yan ƙasar suka warwatsu a faɗin duniya.
A Amurka, garin Minneapolis wata mattara ce ga 'yan Somalia, za a iya cewa a nan ne 'yan Somalia masu zama a ƙasashen duniya suka fi yawa.
Tun bayan lamarin da ya faru na Satumbar 2001, ana ta ce-ce-ku-ce kan makomar musulmai a Amurka. Mista Trump na yawan amfani da wasu kalamai na ƙin jinin musulunci domin kwatanta 'yan ci rani marasa bin doka wanda hakan ke sa tsoro a cikin zukata.

Asalin hoton, Getty Images
Ga Mista Trump, Ms Omar ba ta shiga cikin tsarinsa na "'yan ci rani na kirki" ba. 'Yar majalisar mai saka hijabin ta nemi 'yancinta na saka hijabi a majalisar wakilan ƙasar, inda ta kawo ƙarshen abin da aka haramta na shekaru 181.
Ba ta tsoro wai don ita musulma ce - wannan shi ne abin da ya bambanta ta da sauran mata musulmai na Amurka.











