Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zargin Hushpuppi: 'Yan sandan Dubai sun miƙa Hushpuppi ga FBI ta Amurka
Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta miƙa dan Najeriyar nan da ake zargi da damfara, Raymond Igbalode Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, ga hukumar bincike ta FBI a Amurka.
'Yan sandan Dubai ne suka sanar da hakan a wani sako da suka wallafa a shafinsu na Twitter.
A makon jiya ne 'yan sandan Dubai suka kama mutane biyu da ake zargi da damfara "Hushpuppi" da "Woodberry" da wasu Amurkawa 10 'yan damfara ta intanet a wani samame na musamman da suka kira "Fox Hunt 2".
A samamen aka kama mutanen biyu kan aikata munanan laifuka a UAE da suka hada da halatta kudi haram da zamba ta intanet, da kutse da yin sojan gona don aikata laifi da makamantansu.
Sun kama wadanda ake zargin ne a wasu jerin samame da tawagogin 'yan sanda shida suka yi a Dubai, wadanda suka lalata shirin 'yan damfarar na karbar makudan kudade daga hannun jama'a da yawa a fadin duniya.
Kusan mutane miliyan biyu aka yi amanna sun fada komar dan damfarar.
Shugabana hukumar FBI Christopher Wray ya yabi 'yan sandan Dubai kan wannan gagarumin aiki na kama "Hushpuppi" da Olalekan Jacob Ponle da aka fi sani da "Woodberry" a samamen nasu na "Fox Hunt 2".
Mr Wray ya mika sakon godiyarsa ga 'yan sandan Dubai kan jihadin kan da suka bayar na mika wa Amurka masu laifin da ake zargi da zamba da damfara.