Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hushpuppi: Babban dan damfarar da aka cafke a Dubai
'Yan sanda a Hadaddiyar Daular Larabawa sun cafke wani dan Najeriya da ya yi suna a shafin sada zumunta na Instagram Raymond Igbalodely da aka fi sani da Hushpuppi, kan zargin damfarar Dala miliyan 435.
'Yan sandan sun kuma cafke wasu mutum 11 'yan kungiyar a samamen da suka kira Fox Hunt 2 a samame 6 da suka kai a kasar.
Kusan mutane miliyan biyu akai amanna sun fada komar dan damfarar.
Hushpuppi na zaune ne a Dubai kuma yana takamar shi attajirin dan kasuwa ne.
'Yan sanda Dubai sun wallafa a shafinsu na Twitter yadda suka shafe watanni hudu sun gudanar da bincike a kansa.
Jami'an tsaro sun ce sun gano wannan gungun 'yan damfarar ta hanyar intanet da ke Dubai amma suna ayyukansu a kasashe da dama wajen hallata kudin haram da aikata zamba da dai sauraransu.
Ana zargin gungun da kutse a shafukan intanet na jama'a ta yadda za su kwashe kudin mutane zuwa na su asusun ajiyar.
Kawo yanzu babu karin bayani kan ranar da 'yan sanda a Dubai za su gurfanar da su a gaban kuliya.