'Man fetur ɗin da Najeriya ke sayowa na da guba'

Asalin hoton, Getty Images
Man fetur ɗin kasuwar bayan fage da ake samu a Najeriya ya fi ƙarancin guba a kan mai da dizal ɗin da dillalan Turai ke siyar mata, a cewar wani rahoto.
Ana dai fargabar cewa man da dillalan kayayyaki suke siyar wa Najeriya bayan an tace shi a nahiyar Turai yana shafar ingancin iskar da ake shaƙa a ƙasar mafi yawan jama'a a Afirka.
Wata ƙungiyar masu fafutuka da ake kira Stakeholder Democracy Network (SDN) ta kwatanta samfur 91 na man da ake shigarwa ƙasar da na Najeriya da ake samu a kasuwar bayan fage daga yankin Neja Delta mai arziƙin man fetur.
Nazarinta ya nuna cewa man fetur da dizal ɗin da ake kai wa ƙasar na ƙunshe da sinadarin sulphur sama da ninki 200 fiye da abin da Tarayyar Turai ta ƙayyade.
Idan aka kwatanta, da man fetur ɗin da aka samo daga kasuwar bayan fage a yankin Neja Delta, wanda ke ƙunshe da sinadarin sulphur fiye da ninki 150 kan yadda aka ƙayyade.
Ƙungiyar SDN a yanzu na kira a gudanar da gwaje-gwajen tabbatar da ingancin man fetur ɗin da ke faɗin ƙasar cikin gaggawa don gano ɗaukacin wannan matsala.
A shekara ta 2017, Hukumar Tabbatar da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya ta amince da haɓaka mizani kan ingancin man fetur da ake kai wa ƙasar, sai dai ƙungiyar SDN ta ce ba a yi wani ƙoƙarin a-zo-a-gani ba wajen tabbatar da bin ƙa'idar.
Najeriya dai na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziƙin man fetur a duniya, sai dai matatunta sun rufe ko kuma ba sa aiki yadda ya kamata, abin da ya sa ƙasar ta yi matuƙar raja'a a kan man da ake sarrafa a ƙetare sannan a sake siyar mata











