Matsalar tsaro: Abu biyar da malaman Najeriya suke so Buhari ya yi

Matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya musamman a yankunan arewa maso gabas da kuma arewa masu yamma su ne jigon taron da malaman kasar suka gudanar a karshen mako.

Zauren Malaman, wanda ya hada da malamai masu bin akidu daban-daban, ya yi taro ne ta manhajar Zoom, inda ya yi nazari kan matakan da gwamnatocin baya suka dauka da nasarar da suka samu da kuma wadanda ake dauka yanzu da nasararsu su ma, da kuma gazawar da aka yi a lokaci guda.

Sakataren zauren Malaman, Injiniya Bashir Adamu Aliyu, ya yi wa BBC karin bayani. Ga wasu daga cikin abubuwan da malaman suka tattauna a kai:

1- Matsayar malamai

Bayan nazari kan matsaloli irin na garkuwa da mutane da yaduwar makamai a hannun daidaikun mutane da yadda ake samarwa 'yan ta'adda bayanan sirri da kuma yadda ake halin ko in kula da matsala tun tana karama da dai sauransu.

Ya sanya malaman suka fitar da matsaya cewa tsaro shi ne kashin bayan bunkasar tattalin arziki wanda a kullum ake kuka da tabarbarewarsa, al'umma na bukatar tsaro sama da abinci da ruwan sha har ma da lafiyarsu.

Cikin matsayar malaman sun yi gargadin siyasantar da al'amuran tsaro kai ya haifar da mummunan sakamako ga shugabanni nan gaba da kuma sauran mutane baki daya.

Yayin wannan taro ya yi tir da aikin 'yan ta'adda da kuma kiransu da su aje makamansu domin komawa cikin mutane da ci gaba da rayuwa mai tsafta.

2- Shawarwari ga gwamnati

Cikin shawarwarin sun tunatar da shugabannin cewa ya kamata su yi tsoron Allah su tabbatar da tsaro ga mutanen da suka zabe su da zummar kare rayukansu da dukiyoyinsu, a ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa tare da habbaka ilimi da bangaren lafiya da ke neman durkushe wa.

Ya kamata gwamnatin tarayya ta rika kula da hakkokin jami'an tsaro wadanda suka hada da kula da marasa lafiyarsu da iyalan mamatansu, sannan a rika hukunta wadanda aka tabbatar da cin amanar kasa ko kuma zagon kasa.

NIGERIA PRESIDENCY

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto, Matsalar tsaro na ci wa kowa tuwo a kwarya - in masana

Haka kuma akwai bukatar daukar sabbin jami'an tsaron, a kuma horas da jami'an Civil Defence don taimakawa sauran jami'ai wajen dakile ta'addanci a kasa baki daya.

Malaman sun yi kira ga gwamnatin tarayya da duba kiraye-kirayen da ake mata na yin garambawul cikin shugabancin harkokin tsaro a kasar domin hakan na da matukar alfanu.

Karancin tuntubar mutane kan matsalar na daga cikin koma bayan da ake fuskanta, don haka akwai bukatar samar da wata kafa ta jin shawarwari daga masa da shugabannin al'umma.

Ya kamata a samar da kotu ta musamman da za ta rika daukar matakin gaggawa kan masu garkuwa da mutane da masu yin kisan gilla.

A kara daukar matakan tsaro kan iyakokin Najeriya wanda sakaci kan haka na ba da damar ta'azzarar kwararar muggan mutane ko kuma ficewarsu a lokain da ake nemansu ido rufe.

A kwai bukatar malamai su tashi tsaye wajen fadakar da alumma kan komawa ga ubangiji da jin tsoronsa.

3- Abin da jami'an tsaro ya kamata su yi

bbc
Bayanan hoto, Sojojin da Buratai ke jagoranta na ci gaba da fatattakar 'yan Boko Haram

Kusan shawarwari iri guda ne tsakanin gwamnati da jami'an tsaro, sai dai sun nemi jami'an tsaro su rika kyautatawa duk wani wanda ya yi bajinta lokacin aiki a yakin da suke da bata-gari.

Sun kuma nemi a rika samar da bayanan sirri wanda yana daya daga cikin abubuwa masu mahimmanci a yaki da 'yan ta'adda.

Haka zalika malaman sun nemin a dawo da tsarin (Community Policing) domin samar da bayai ga jami'ai.

Shugabanni su binciki koke-koken da ake game da danne hakkokin kananan ma'aikatansu da ke filin da ga da wadanda ke aikin ba da tsaro a wasu sannan kasar.

Dole kuma su kiyayen sirrin basu basu bayai a yakin da suke yi da ta'addanci a fadin kasar.

4- Al'umma na da rawar da za su taka

Dole mutane a koma ga Allah domin tuba da neman kawo karshen wannan dambarwa da ta ki ci ta ki cinye wa.

Dole a hada kai domin kare kai da ba da hadin kai ga jami'an tsaro.

A guji tsinewa shugabanni, maimakon haka a rika taya su da addu'a.

Al'umma ta guji raina abubuwan da ke faruwa domin tashe kafafen barna da ka iya kunno kai.

5- Malamai da Limamai

Malamai su shaida wa al'umma cewa akwai bukatar su dauki dabi'ar taimakawa juna musamman lokacin da aka tsinci kai cikin wata matsala.

Malamai su rika nusantar da mutane kan yadda za su rika yiwa shugabanni addu'a maimakon tsine musu saboda tsinuwar na dawowa ne kan daidaikun mutane a karshe.

MBuhari Twitter

Asalin hoton, MBuhari Twitter

Bayanan hoto, Malaman sun bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara kaimi a kokarinsa na magance matsalar tsaro

Dole malamai su rika tunatar da shugabannin kan sauke hakkokin da ke kansu da kuma sanin cewa za a tambaye su ko sun sauke a gobe kiyama.

Malami su daina sanya son zuciya wajen karantar da dalibai domin daga nan ne tushen gurbacewar tarbiyya da aƙida ke samo asali.

Kungiyoyin addini su kara duba lamarin tura masu yaɗa addini cikin kauyuka sako da lungu.

Malamai su rika kiyaye harsunansu wajen bayani duk lokacin da wani abu ya faru, kada su rika kausasa harshe, domin daga na gaba ake ganin zurfin ruwa in ji hausawa.

An kwashe kimanin kwana tara ana gudanar da wannan taro ta kafar intanet sakamakon annobar korona da ta hana haduwa fuska da fuska.

Farfesoshi da Daktoci Baristoci da dai sauran manyan malamai duk sun halarci taron.