Ajimobi: Surukin Ganduje kuma tsohon gwamnan Oyo ya mutu

Ajimobi

Asalin hoton, TTWITTER/@AAAJIMOB

Allah Ya yi wa tsohon gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya Sanata Abiola Ajimobi rasuwa a ranar Alhamis da yamma.

Wani makusancin sanatan ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar tasa.

Sanata Ajimobi wanda ya yi gwamnan Oyo na tsawon shekara takwas ya rasu yana da shekara 70 a duniya.

Tuni wasu makusantansa suka fara wallafa sakonnin ta'aziyyar rasuwar tasa a shafukan sada zumunta. Rahotanni sun ce ya rasu ne a wani asibiti a birnin Legas bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Short presentational grey line

Wane ne Sanata Ajimobi

Sanata Abiola Ajimobi shi ne tsohon gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 2011 - 2019.

Kafin ya zama gwamnan jihar Oyo ya rike mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai a 2003.

Amma Sanata Ajimobi ya fadi zaben kujerar majalisar dattawa ta Kudancin Oyo inda abokin karawarsa na jam'iyyar PDP Kola Balogun ya kayar da shi a 2019.

Ya mutu ya bar mace daya Florence Ajimobi da kuma yara biyar. Daya daga cikin 'ya'yansa Idris Ajimobi ya auri 'yar gidan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Fatima.

A ranar 18 ga watan Yunin nan aka yi ta yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan ya mutu, har sai da surukar tasa Fatima Ganduje ta karyata hakan a shafinta na sada zumunta.

A wata hira da mai magana da yawunsa Bolaji Tunji ya yi da Sashen BBC Yoruba ranar 16 ga watan Yunin 2020, ya ce Ajimobi zai warware dukkan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC.

Kuma a lokacin Mista Tunji ya ce an yi ta yada jita-jitar mutuwarsa ne sakamakon dogon suma da ya yi a asibiti.

Wannan layi ne
Wannan layi ne