Me ya sa mutuwar miji kan jefa mata cikin garari?

Mutuwar miji na da rikitarwa sai dai wasu al'adu da ke biyo bayan rashin mijin a sassan duniya na jefa rayuwar mace da ke zawarci cikin kunci - musamman ma idan aka tabo batun da ya shafi abinci, a cewar Emily Thomas.

A wasu al'adun ana hana macen da ke zawarci cin abinci a lokutan da suka dace, haramta mata cin abinci mai gina jiki, da kuma tilasta mata aiwatar da wasu al'adu masu hadari kan cin abinci.

A Ghana, bazawara da ke cikin talauci ta fi shiga azaba. Yayin da kasar ke kokarin kawo karshen rashin ganin daraja da wasu al'adu masu hadari da ake tilastawa mata su yi a lokacin makokin mijinsu, har yanzu akwai zawarawa da ake hanawa cin abinci mai gina jiki - ko sama da hakan ma.

Akwai al'adar da ke tilastawa bazawara shan miyan da aka yi da wani sassa na jikin mijinta da ya rasu.

''Ana amfani da gashi ko farcen miji, ana yi wa gawarsa wanka sannan a bai wa mace ruwan ta sha,'' a cewar Fati Abdulai, darakta a wata kungiya da ke kare hakkin zawarawa da marayu a arewacin Ghana.

Wasu zawarawan na iya kalubantar wannan cin zarafi ko su bijirewa al'adar - amma wasu musamman talakawa ba sa iya wa.

Sannan da yake a wasu al'adun dukiyar miji na koma wa hannu 'yan uwansa idan ya mutu, mata da dama na rasa dukiyoyi da filaye - sai dai idan sun amince su auri daya daga cikin 'yan uwan mijin da ya rasu.

An kiyasta cewa a duniya akwai mata miliyan 285 da ke rayuwar zawarci, sannan mutum daya cikin 10 na cikin matsanancin talauci.

A kasashe da dama, matar da ta rasa mijinta ana kyamatarta ga kuma gori - Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cin zarafin da ake yi wa zawarawa a matsayin keta hakki mafi muni na rayuwa.

''Haramci kan kifi, nama da kwai''

A wasu yankunan duniya tsangwamar da ke tattare da zawarci ba a kan matalauta kawai ta tsaya ba har yankunan da mutane ke tunkahon arziki.

A cewar Chitrita Banger Gee, wata masaniyar tarihi da ke rubuta litattafai, a kabilar Hindu a yammacin Bengal, a shekarun baya a kan tilastawa zawarawa su yi bayanin yadda suka kashe mazajensu.

''A kan haramta musu cin kifi da nama da kwai da albasa da tafarnuwa - cikin irin wannan al'ada suka rayu kafin daga bisani al'adar ta gushe,'' a cewar Gee.

''Abin da ake kokarin aiwatarwa shi ne hana su cin abinci mai gina jiki - kamar laifin matan ne, wato ta aikata zunubi kenan, ana azabtar da ita - ana cimma wannan nasara ce ta hanyar hana ta abinci.''

Wannan wani yanayi ne da Gee ta taba shaidawa ta na karama, lokacin da mijin kakarta ya rasu.

''A wurina wani sabon sauyi ne - ta sauya kayan da take sanyawa daga tufafi masu kala zuwa fari babu batun amfani da sarkoki ko dan kune. Ta daina cin abinci da 'yan uwa kuma ba komai take ci ba, saboda akwai abincin da aka haramta mata.''

''Amma idan ta yi girki, wasu abincin nata akwai dadi sosai.''

A matsayinta na masaniya kan abinci, Banger Gee ta ga yadda kakarta ta sauya abincin da aka haramta mata da kayan dandano.

''Ba ta cin albasa, don haka sai ta yi amfani da wanda aka sarrafa ko abin da zai ba ta irin wannan armashin a girki,'' a cewar Gee.

Duk inda muka je a duniya, idan muna cikin jimami, muna bukatar abinci mai lafiya da kwantar da hankali. Amma rasa mutumin da muke yawan cin abinci tare abu ne mai wahalar gaske - yana da rikitarwa da shafar lafiyar kwakwalwa.

Wani bincike da aka aiwatar a China, Turai da Amurka, ya gano cewa tsakanin mutane masu shekaru, zawarci na lalata mutum ne saboda rashin abinci mai lafiya da inganci, hakan kuma na sa rama.

Elisabeth Vesnaver, da ke bincike kan abinci mai gina jiki, ta yi nazari mai zurfi kan abincin da zawarawa ke ci a Canada wayanda shekarunsu ke tsakanin 70 zuwa 80.

''Ina da kakani biyu kuma kowace da yanayin da ta tsinci kanta,'' a cewar Vesnaver.

''Daya bayan mutuwar mijinta, cikin shekaru biyu ta mutu kuma babu wata cuta da aka danganta wacce ita ce sanadi mutuwarta, kawai abin da aka gano shi ne cimakarta.

Kalubale ko Tasiri

Vesnaver ta gano cewa irin wadanan zawarawa na fuskantar kalubalen mutuwa a shekarun biyu farko bayan mutuwar mijinsu. Ana samun karuwar mace-mace, sannan tana da yardar cewa abinci na tasiri wajen haddasa mutuwar.

''Haka nan bincike ya nuna cewa abinci da yanayin cin abincin na tasiri a rayuwar zawarci,'' a cewar Vesnaver.''

''Mun shaidi karuwar cin abinci marasa inganci, ramar da ba a shiryawa ba, da rashin jindadi. Sannan maza tsoffi sun koyi girki da ciyar da kan su.''

Ta kara da cewa abin bai tsaya kawai a kan komawa tamkar wanda ciwon yunwa ya kama ba.

''Wani abun mamaki game da mata shi ne kowacce da irin yanayin da ta shiga ko abin da ta fahimta dangane da rayuwa ko yanayi da ma tasirinsa.''

Daya daga cikin irin wannan mata ta shaidawa wasu bincike cewa lokacin da mijinta ya mutu, ba ta da dalilin motsawa ko tashi daga gado. Tana iya shafe tsawon wuni ko daga 11 na safe har 3 na yamma a kwance, batun abinci kuwa sai yadda hali ya yi.

Ta ya ya za a iya taimakwa mutane da ke zawarci?

Lisa Kolb, marubuciya ce kuma tsohuwar jami'a da ke rayuwa a Washington DC, ta bada wasu shawarwari. Ta rasa mijinta Erik a wani hadari watannin 19 da aurensu. Shekarunsu 34 kowanne a wannan lokacin.

''Tare da mijinka sai kuyi girki tare, cin abinci tare, tafiya taruka da wurin chashewa - idan ka rasa wannan kuma to ka shiga kadaici, sannan zama kai kadai a teburin cin abinci babu miji da ka saba da shi akwai wahala,'' a cewarta.

''Duk da cewa cin abinci na da muhimmanci, zama tare da mutane a ci abincin ya fi dadi. Amma wanda ya shiga wannan yanayin kadai ne zai fahimci hakan.''

These interviews featured on an award-winning episode of The Food Chain Widowed: Food after loss on BBC World Service.