Donald Trump: Mutanen da sabuwar dokar bizarsa za ta shafa

US President Donald Trump arrives at a campaign rally at the BOK Center, June 20, 2020 in Tulsa, Oklahoma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump ya yi alkawarin sanya tsauraran dokokin ba da biza a lokacin yakin neman zabensa

Shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita lokacin bayar da takardar zaman dan kasa ta green card tare da dakatar da bayar da biza ga ma'aikata 'yan kasashen waje har sai karshen 2020.

Wannan doka za ta shafi manyan kwararru a bangaren fasaha da wadanda ke taimaka wa ma'aikatan da raino ko ayyukan gida har da ma manyan ma'aikatan kamfanoni.

Fadar White House ta ce matakin zai ba da damar samar da ayyukan yi ga Amurkawan da annobar cutar korona ta shafi tattalin arzikinsu.

Amma masu suka sun ce Fadar White House na amfani da annobar cutar korona wajen tsananta dokokin shigar baki kasar.

Su wa abin ya shafa?

A wani jawabi da aka gabatar wa manema labarai, gwamnatin ta ce dakatarwar, wacce za ta kai har karshen shekarar nan tana aiki, za ta shafi mutum 525,000.

Hakan ya hada da mutum 170,000 da aka kiyasta wadanda matakin ya shafi ba su takardar zama 'yan kasa. A watan Afrilu ne gwamnatin Amurka ta fara sanar da dakatar da ba da bizar, matakin da ya kamata ya kawo karshe a ranar Litinin.

Amma matakin ba zai shafi wadanda a halin yanzu suke da biza ba.

Matakin zai kuma shafi masu rukunin biza H-1B, wadanda da yawan masu irin ta kwararrun ma'aikatan fasaha ne 'yan Indiya. Masu suka sun ce wannan bizar ta bayar da dama ga kamfanonin sadarwa su rika biyan 'yan kasashen waje kudi kalilan don yin aikin da Amurkawa ne ya kamata su yi.

A shekarar da ta gabata an samu mutum 225,000 da suka nemi bizar sai dai gurbin mutum 85,000 ne kawai aka samar a tsarin bizar ta H1-B.

Dokar za ta kuma dakatar da biza rukunin H-2B ga ma'aiaktan da suka hada da bangaren fanninbude ido, sai dai wadanda suke bangaren noma da sarrafa abinci da kwararru a fannin lafiya.

Dokar za ta shafi rukunin biza ta gajeren zango ta J-1 short-term, wani rukuni da ya shafi daliban jami'a da masu taimaka wa ma'aikata ta fannin raino ko kula da gida. Ba a sanya farfesoshi da malamai a cikin dokar ba.

Za kuma a dakatar da biza rukuninL visas da ake bai wa manyan ma'aikata na kamfanonin kasashen waje.

Me ake cewa?

Wani babban jami'i ya ce manufar wannan mataki ita ce don ''a samu moriya a tattalin arziki da ci gaba mai kyau.''

Amma Kungiyar Fararen Hula Ta Amurka ta ce: ''Ana amfani ne kawai da annobar don sauya matakan bai wa baki izinin shiga kasar.''

Sannan manyan kamfanoni ma sun soki wannan dokar, wadanda yawanci sun dogara ne kan ma'aikata 'yan kasashen waje.

Cibiyar Kasuwanci ta ce: "A yayin da ake samun koma baya a tattalin arziki, kamfanoni a Amurka za su bukaci a ba su tabbaci cewar za su iya samun dukkan ma'aikatan da suke bukata.''