Jam'iyyar APC: Ko za a iya ɗinke ɓarakar da ta kunno kai a cikinta?

Wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya sun bayyana takaicinsu kan yadda rikicin cikin-gida yake neman wargaza ta.

Lamarin na faruwa ne bayan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya fice daga jam'iyyar sakamakon takaddamar da ke tsakaninsa da shugabanta da kotu ta dakatar, Mr Adams Oshiomhole.

Hakan ya sa jam'iyyar ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo wanda shi ne shugabanta na yankin kudancin kasar, Abiola Ajimobi, a matsayin shugaban riƙo na jam'iyyar APC. Amma wani fitaccen dan jam'iyyar Victor Giadom ya samu izini daga kotu cewa ya shugabanci jam'iyyar a matsayin riƙo, lamarin da masu fashin bakin siyasa suka ce zai hana jam'iyyar lashe zaben 2023 idan ba ta dinke barakar ba.

Jam'iyyar ta sauka daga kan aƙidu na dimokuraɗiyya

Faruk Adamu Aliyu wanda jigo ne a jam'iyyar APC ya ce da dama 'yan jam'iyyar irinsu na takaicin irin wutar da ke ci a cikin jam'iyyar mai mulki.

Sai dai ya ce Shugaba Buhari ya bayar da umarni fara aikin dinke barakar ta hanyar zama da sasantawa tsakanin wadanda aka batawa.

Wannan dai na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da tsohon shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Edo inda wutar rikicin jam'iyyar a yanzu haka ke ruruwa, John Oyegun, ya yi gargadin cewa "rikicin da jam'iyyar ke fama da shi a jihar Edo na barzana ga shugaba Muhammadu Buhari."

A cikin wata maƙala da ya yi wa taken "Before It Is Too Late" wato "Kafin a Makara", da jaridun Najeriya suka wallafa, Oyegun ya yi kira ga Buhari da kuma gwamnoni da su kawo ƙarshen abin da ya kira "abin kunya" da ke faruwa a sakatariyar jam'iyyar.

"Jam'iyyarmu ta APC na ta yin ƙoƙarin kawo wa ayyukan gwamnatinmu da shugabanmu barazana," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "A 'yan watannin da suka gabata, mun ga yadda jam'iyyar ta sauka daga kan aƙidu na dimokuraɗiyya, abin da ya sa duk waɗanda suka yi zaton ganin alƙawarin sauyin da ta yi musu suka zarge ta da munafurci.

"Saboda haka wajibi ne mu riƙa tunawa cewa nasarar da muka yi a shekarar 2015 da kuma karɓar mulki cikin ruwan sanyi wani gwaji ne da ke nuna matuƙar ci gaba game da dimokuraɗiyya a ƙasarmu."

'Shugaba Buhari ya makaro'

Masu fashin bakin siyasa na ganin beken shugaba Muhamamdu Buhari dangane da yadda rikicin jam'iyyar APC ya ki ci ya ki cinyewa, al'amarin da ya haifar da bangarori biyu kowanne na ikrarin shugabancin jam'iyyar.

Sai dai 'yan jam'iyyar shugaban irin su Farouk Adamu Aliyu na cewa Muhammadu Buhari mutum ne da ba ya son katsalanda a al'amuran siyasa.

Malam Elharoon Muhammad, malamai a Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna ya ce " Shugaba Buhari bai so kashe wutar rikicin nan ba kasancewar shi ne jagoran jam'iyya kuma shugaban Najeriya wanda zai iya tsawatarwa kowa."

Dangane da yunkurin shugaba Buharin na ganin an sasanta 'ya'yan jam'iyyar, Malam Elharoon ya ce " an makaro kasancewar an bar rikicin ya riga ya yi nisa ba tare da tsawatarwa ba. Yanzu haka bangarori biyu suna ikrarin shugabancin jam'iyya ka ga abu ya baci kenan"

Ina makomar APC?

Malam Elharoon Muhamamd ya ce "makomar jam'iyyar APC ba wata mai kyau ba ce bisa dogaro da irin jihohin da ta rasa a zaben da aka yi na 2019. Sannan yanzu ma ta sake rasa gwamnan jihar Edo wanda ya sauya sheka zuwa PDP kuma tuni sun ba shi takara."

Bayanai dai na nuna cewa tun bayan hawan Adams Oshiomole kan karagar jam'iyyar APC kawo yanzu, jam'iyyar wadda a baya take da jihohi 24 ta koma yin kankankan da jam'iyyar hamayya ta PDP.

Yanzu dai APC na da jihohi 18, inda ita kuma jam'iyyar PDP ke da 17 ciki har da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki wanda ya sauya sheka a makon da ya gabata.

Shi ma Dr Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja, yayin shirin Ra'ayi Riga na BBC, ya shaida cewa "wadannan rikice-rikice da jam'iyyar APC ke fama da su ba sa rasa nasaba da shirye-shiryen zaben 2023."

Ya kuma kara da cewa "idan dai har ba a yi wa tufkar hanci ba to jam'iyyar za ta dare ne kuma bai zama lallai ta samu abin da take so ba a 2023."

Sai dai Faruk Adamu Aliyu wanda jigo ne a jam'iyyar ta APC, ya yi inkarin hasashen masanan inda ya ce "ba za ka hana mutum hasashe ba amma mu dama mun san cewa za a kai ga wannan gaba kasancewar jam'iyyar APC hadaka ce tsakanin jam'iyyu fiye da biyar. Ka ga kenan kowa ya shiga jam'iyyar ne da irin halayyarsa."

Me ya haifar da rikicin da APC ke ciki yanzu?

Farouk Adamu Aliyu ya ce abubuwa da dama sun faru da suka hada da kin amincewa a gudanar da zabukan wasu mukamai a jam'iyyar.

Sai dai ya ce abu na baya-bayan nan shi ne kokarin shugaban jam'iyya na kasa na hana gwamnan jihar Edo yin takara.

Tun dai bayan da shugaban jam'iyyar ta APC da kotu ta dakatar, Adams Oshiomole ya fahimci gwamnan jiharsa ta Edo Godwin Obaseki ya fara yi masa tawaye, sai Oshiomole ya fara tunanin hana gwamnan jihar tasa neman takara a karo na biyu, in ji Farouk Adamu Aliyu.

Al'amarin ya yi kamari ne lokacin da jam'iyyar APC ta ce takardun karatun gwamna Obaseki ba sahihai ba ne, inda ta ce bai cancanci tsayawa takarar cikin gida ba da za a yi ranar 22 ga watan Yunin nan.

Shi ma kuma gwamna Obaseki ya yi amfani da karfin ikonsa a jihar, inda shugabannin jam'iyyar APC na rumfar zaben Adams Oshiomole suka ce sun dakatar da shugaban jam'iyyar APC din na kasa.

Dama kuma akwai wata shari'a a kasa da wata kotu ta dakatar da Adams Oshiomole daga kujerar shugabancin APC bisa zargin yi wa dokokin jam'iyyar karan tsaye, inda a makon da ya gabata kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin.

Wannan al'amarin ne dai ya haifar da bangarori biyu na jam'iyyar ke ikrarin shugabancin jam'iyyar na rikon kwarya.

Masana dai na ganin Adams Oshiomole ya yi kokarin kwaikwayar Bola Ahmed Tinubu wanda ya yi duk mai yiwuwa wajen hana tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode sake takara.

To sai dai kasancewar Bola Tinubu wani mutum da yake rike da akalar siyasar Legas, Ambode bai iya yi masa tawaye ba, sabanin Adams Oshiomole wanda masana ke yi wa kallon Gwamna Obaseki ya karbe iko da jihar.

Wannan rikici da jam'iyyar mai mulki ke ciki yanzu haka, a cewar Malam Elharoon Muhammad "na da tasiri ga shugabancin Najeriya ta fuskar tsaron kasa da tattalin arziki da ma uwa uba aminci tsakanin shugabannin da talakawa."

Karin labarasi da za ku so ku karanta: