Yadda fina-finai kan Michelle Obama da Hillary Clinton suke ƙarfafa gwiwar mata

    • Marubuci, Daga Emma Jones
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Entertainment reporter

Fim ɗin Becoming Michelle Obama ya zama daya daga cikin fina-finan da aka fi kalla a shafin nuna fina-finai na intanet Netflix bayan fitar da shi a makonnin baya, yanzu kuma wata mai dakin tsohon shugaban kasar Amurkan, Hillary Clinton ta fitar da nata fim ɗin kan tarihin rayuwarta.

Fim ɗin na kimanin sa'a hudu, ya hadar da wata tattaunawa da Clinton ta yi da matar da ta shirya shirin Nanette Burstein, wadda ta bayyana tsarin rayuwar Hillary Rodham Clinton daga fara gwagwarmayarta a 1960, zuwa aurenta da tsohon shuagaban kasar Bill Clinton, labarin rikicin Monica Lewinsky da kuma kokarinta da bai yi nasara ba na zama shugabar Amurka a 2016.

Hillary ta dage cewa matan da za su shugabanci kasar za su samu kwarin gwiwa ne daga kayen da ta sha a zaben 2016, da kuma zaben majalisa na 2018; da aka kafa tarihin zabar mata 103, ciki har da irin su Alexandria Ocasio-Cortez.

"Na san matsayi na a wajen mata da yawa, ina jin yadda suke fadin cewa sun samu kwarin gwiwa daga gare ni kusan kullum," Clinton ta shaida wa BBC. "Ba karamin nauyi ba ne."

"Na yi kokarin bayyana matsayata wajen tabbatar da wace ce ni kuma abin da nake so, amma har yanzu muna bukatar wata mace abar koyi, wadda za mu rika kallo muna jarraba sa'armu, matukar wani zai iya to ai ni ma zan iya kenan - irin wannan tunanin ake so a rika yi kuma na san akwai masu yin sa da dama."

A cikin Fim din Becoming na mai dakin tsohon shugaban Amurka Michelle Obama wanda ta zagaya wasu kasashen duniya domin tallata shi, da kuma yadda ta hadu da matasan mata bakar fata 'yan Afrika tare da karfafa musu gwiwa kan burinsu. Wadda ta shirya shirin Nadia Hallgren ta ce ba ta taɓa ganin yadda aka ba da kwarin gwiwa ba kamar wannan ba.

"Mene ne mata ke fatan ganin an kira su da shi?, in ji Hallgren, "a labarinta an nuna ba zai yiwu a ce ba za ka iya komai ba, ko kuma kai kullum a baya kake a rayuwa. Tunanin shi ne kawai idan ke mace ce to ke ba namiji ba ce.

"Ina ganin akwai yunwa da yawa a fadin duniya kamar inda aka fadi a labarinta. Na ji Misis Obama na magana kan matsalolin da ake fuskanta da kuma yadda ake shawon kansu a rayuwa, kuma ga yadda za ka iya aiwatar da hakan, ni kaina ya taimakan sosai a tawa rayuwar."

Nanette Burstein, wadda ita ta shirya fim din Hillary ta ce, wannan yunkuri na wadannan mata yana da matukar amfani "musamman ga matasa".

"Kuma wani karin abin jin dadin shi ne duka fina-finan mata ne suka shirya su, tana nuna wadda ta shirya Brids Eye Mia Bays lokacin da take maganar.

"Fim din ya taimaka mana wajen gano dalilin da ya sanya Michelle ta zama mai ba da kwarin gwiwa ga mutane, da kuma wajibin da ke da akwai kan wadanda suka yi nasara su taimaka wa wadanda ke kasa musamman a yanzu."

Idan aka kwatanta, a wajen mata, Hillary Clinton tun a baya ta zama wata abar yin ja-in-ja a kanta a 2016, inda wani bincike ya nuna mata kimanin kaso 52 cikin 100 ne suka zabe ta, kashi 64 cikin 100 kuma wadanda basu je makatranta ba ne, fararen mata kuma suka zabi Donald Trump.

Clinton ta ce tana sane da kiyayyar da ta janyowa kanta.

"Abin mamaki ne a so ka, amma idan abin da kake so kenan, to kaga ba ka fito bane domin yin abin da ya kamata. Akwai wasu dauka da na manta da su a cikin wannan fim.

"Ina yaki ne game da tsarin kiwon lafiya, amma mutane na yaƙar karsashi na ba sa so na, ba kuma sa son abin da nake yi ba sa sona ne domin suna da wanda suke so a zuciyarsu.

"Lokacin da mace ke kokarin rike wani matsayi na al'umma, to dole ta shirya da shan suka, amma idan ba ta shirya ba, kada ta ma fara tun karar shirin. Ina matukar alfahari da abin da na yi da kuma matsayi na, ba kuma na nadamar komai a kai."

Clinton ta yi amannar irin wadannan fina-finan wata hanya ce ta kafa tarihi kai tsaye.

"An ta yaɗa labarukan karya a kaina, an ta ɓatan suna - amma da wannan fim din na nuna yadda rayuwa ta ya kamata a fahimce ta wanda kuma abu ne mai kyau." a cewarta.

'Ba zaki taɓa hutawa ba'

"Na yi amannar sai na fuskanci suka kan yadda aka tsara wannan labari," in ji wadda ta shirya Nanette Burstein. "Na san ko me na yi duk kyansa sai an soka. To dan haka na ji ya kamata na yi bincike kuma na tsaya kan gaskiya iya iyawa ta."

Hillary Clinton ta ce mata na bukatar a kara karfafa musu gwiwa kan abin da ya shafi shugabanci na gari - ko dai a kafofin yaɗa labarai, ko a masana'antar shirya fina-finai ko kuma a siyasa.

"Ina ganin ta hanyar bayyana labari na, za a samu sauyi sosai, amma za kaga yadda za a kyamaci abin da kuma irin maganganun da zai janyo," in ji ta.

Don haka ba zaki taba hutawa ba, kuma dole ka ji ka gaji da zama mai gaskiya. me yasa har yanzu mutane ba sa nuna jin dadi da kuma martaba gudunmawar mata?

"Don haka ki sani, za a ci gaba da fafutuka."