Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
John Bolton: Trump ya nemi China ta taimake shi ya sake yin nasara a zaɓe
Shugaban Amurka Donald Trump ya nemi taimako daga wurin shugaban China Xi Jinping domin ya sake lashe zabe, a cewar sabon littafin da tsohon mai bai wa shugaban shawara kan sha'anin tsaro John Bolton.
Mr Bolton ya ce Mr Trump yana so China ta sayi amfanin gona daga wurin manoman Amurka, a cewar littafin da zai fito nan gaba wanda kafofin watsa labaran Amurka suka yi sharhi a kansa.
Ya kara da cewa Mr Trump "bai san komai ba kan yadda za a tafiyar da fadar White House".
Gwamnatin Trump tana ta kokarin ganin littafin bai fita kasuwa ba.
A tattaunawarsa da Fox News, Mr Trump ya ce Mr Bolton: "Ya karya doka. Wannan bayani ne na sirri da bai kamata ya fito fili ba kuma ba shi da izinin fitar da shi."
"Mutum ne maras kan gado," in ji shugaban kasar inda ya kara da cewa "na ba shi dama."
John Bolton ya zama mai bai wa shugaba kasa shawara kan sha'anin tsaro a watan Afrilun 2018 sannan ya ajiye aiki a watan Satumbar 2019. Amma Shugaba Trump ya ce korar Mr Bolton ya yi saboda ba ya bin "muradu" irin nasa.
Ya yi suna wajen tsattsauran ra'ayi game da shirin kasar kan harkokin kasashen waje kuma ya taba yin aiki a gwamnatin Shugaba George W Bush. A matsayinsa na mai bai wa shugaba kasa shawara kan sha'anin tsaro, shi ne babban mai bayar da shawara ga shugaban Amurka kan harkokin tsaro a ciki da wajen kasar.
Littafin na Mr Bolton mai shafi 577, mai suna The Room Where It Happened, zai fita kasuwa ranar 23 ga watan Yuni.
Ranar Laraba da daddare, ma'aikatar shari'ar Amurka ta nemi kotu ta hana fitar da littafin.
Kamfanin da ya buga littafin, Simon & Schuster, ya fitar da sanarwar da ke cewa: "Matakin da gwamnati ta dauka a daren nan na rashin kan gado ne, cike da siyasa wanda ba zai yi tasiri ba."
Ya ce tuni aka rarraba dubban kwafe-kwafe na littafin ga kasashen duniya kuma matakin da ke son hana fitar da shi ba zai cimma komai ba.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Democrat a zaben da za a yi a watan Nuwamba, Joe Biden, ya fitar da sanarwa game da littafin inda ya ce: "Idan har abubuwan da ke cikin littafin gaskiya ne, ba kawai rashin ya kamata ba ne kawai, batu ne da ke nuna cewa Donald Trump ya keta rantsuwar da ya sha ta bautawa Amurkawa."