Coronavirus a Afrika Ta Kudu: An bukaci gwamnati ta sake haramta sayar da giya

Shugaban hamayya na Afrika Ta Kudu Julius Malema ya yi kira ga gwamnati da ta dawo da haramcin da ta sanya kan barasa a lokacin kullen cutar korona.

Shugaban jam'iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), yana caccakar matakin Shugaba Cyril Ramaphosa ne na bude harkokin kasuwanci a wani jawabi da ya gabatar na murnar Ranar Matasa Ta Afrika Ta Kudu.

Afrika Ta Kudu ta shafe wata biyu cikin kullen cutar korona mafi tsauri a duniya - inda har aka dakatar da sayar da giya.

Ana ganin matakin zai rage cin zarafi da ke faruwa a gidajen aure, da hana tashe-tahsen hankula da kuma saukaka wa asibitoci yanayin da suke ciki a lokacin kulle.

An alakanta yawan aikata laifuka da dage haramcin sayar da giyar da aka yi a ranar 1 ga watan Yuni.

"Mun yi kira da a sake duba dage haramcin sayar da barsa, don kare rayuwar al'umma fiye da ribar da za a samu,'' kamar yadda Malema ya fada aranar Talata.

"Shugaban kasa da kansa ya bari a sayar da giya a kasar da take da tarihin yawan mace-mace da samun marasa lafiya sakamakon rikice-rikicen da shan barasa ke jawowa.''

Mr Malema ya ce za a dora alhakin mace-macen da ke da alaka da shan barasa a kan Shugaba Ramaposa ya kuma zargi shugaban da zama abokan Turawan da suka mamaye tare da juya ragamar kasar.''

Shugaban jam'iyyar ta EFF a baya ya nuna adawa da sake bude makarantu da wuraren ibada da aka yi.

Afrika Ta Kudu ta sake bude makarantu ne ga daliban shekarar karshe a ranar 8 ga watan Yuni, amma tuni aka sake rufe makarantu da dama da a baya aka bude bayan samun karuwar masu dauke da cutar korona.