Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙwayayen da wata mata ta saya a kanti sun ƙyanƙyashe agwagi
Ƙwan da wata mata ta saya a kanti a Burtaniya sun ƙyanƙyashe sun zama ƴan tsaki uku.
Matar mai suna Charli Lello da ke zaune a Hertfordshire ta sayo ƙwan ne ta kuma sanya su a injin ƙyanƙyasa don gwaji a ƙoƙarinta na magance zaman zaman kadaici.
Ta ce za ta kiwata ƴan tsakin agwagin tare da jain da take kiwo.
Wani mai magana da yawun kantin ya ce babu wani hadari a cin ƙwayayen da zakara ya bi kaza ta yi kuma ba za a iya gane bambancin su da sauran ƙwayaye ba sai an saka su a injin ƙyanƙyasa.
Ms Lello ta ce ta samu basirar yin hakan ne bayan da ta ga wani bidiyo a Facebook inda wani mutum ya ƙyanƙyashe ƙwan salwa da ya saya a kanti.
"Lokacin da na shiga kantin sai na ga ƙwan agwagwar na kuma yi tunanin cewa su ma za su iya ƙyanƙyashewa. Na ji dadi sosai da suka ƙyanƙyashe amma har yanzu a raina ina saka cewa ƙwan kanti ne.''
Wata guda bayan haka ta sanya su a injin ƙyanƙyasa, Ms Lello ta yi ta jin ƴar kara haka daga baya sai ƙwayayen suka fara fita daga bawonsu.
Ta ce ƙyanƙyashe ƙwan ba abu ne mai sauƙi ba.
"Abin da ya sa na gwada yin hakan saboda ina dan hutu ne don haka ina da lokacin kula da ƙyanƙyasarsy. Amma in ba don haka ba ba abu ne mai sauƙi ba ƙyanƙyasar tasu," a cewarta.