'Ƴan Biafra na amfani da Kiristanci don yaƙar Najeriya - Buhari

Gwamnatin Najeriya ta ce masu fafutikar kafa ƙasar Biafra wadanda kuma ke ikirarin yahudanci suna amfani da addinin Kirista domin kaddamar da yaki a Najeriya.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce ƙungiyar IPOB na farfagandar ƙarya ga ƙasashen duniya kan yadda ake ƙuntatawa kiristoci a Najeriya.

A cewar sanarwar da Malam Garba Shehu mai taimakawa shugaba Buhari kan watsa labarai ya fitar, ta ce "kungiyoyin na fake wa da addinin Kirista - suna kira ga Amurka ta turo manzo na musamman don hana kisan da ake yi wa kiristoci a Najeriya."

Ya ƙara da cewa, "babbar manufarsu shi ne haifar da sabani tsakanin gwamnatin Najeriya da Amurka da Birtaniya da kuma aminan Najeriya na kasashen Turai,"

Babu dai wani martani da ya fito daga bangaren ƙungiyar IPOB game da sanarwar ta gwamnatin Najeriya.

A cikin sanarwar, gwamnatin Najeriya ta yi kira ga 'yan kasa da kasashen duniya su yi watsi da bin da ta kira farfaganda inda ta ce wasu hujjoji sun nuna cewa kungiyar na samun tallafin dalar Amurka 85,000 duk wata tun daga watan Oktoban 2019.

Sai dai gwamnatin ta ce har yanzu ba ta gano wanda ke bayar da tallafin ba.

Ta ce farfagandar ta shafi yin rubuce-rubuce da sunan wasu shugabannin wata kungiyar Kirista da suka kulla yarjejeniya da wani kamfanin Amurka har zuwa ga wasu 'yan majalisa da kuma Fadar White House.

"Abin takaici har an shawo kan wasu daga cikin 'yan majalisar cewa ana cin zarafin Kiristoci a Najeriya - suna bayar da misali da farfagndar kuma har sun dauki maganar zuwa Fadar White House domin nada manzo na musamman."

Ta kuma ce sun yi hayar wasu kamfanoni guda hudu a Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran mambobin kasaashen Tarayyar Turai domin yada farfagandar da suke yi kan Kiristoci a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ce IPOB na amfani da farfagandar a Amurka da kasashen Turai da sunan Kiristoci domin biyan bukatunsu na siyasa.

Ta kuma ce kungiyar na neman lalata tattaunawa tsakanin addinai a Najeriya da kuma bata sunan Najeriya a idon kasashen waje.

A 2017 ne gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biafra a matsayin ta ƴan ta'adda.

An dade dai ana zaman zullumi a yankin Kudu maso gabashiin Najeriya, inda aka samu hatsaniya tsakanin ƴan kungiyar neman kafa kasar Biafra ta IPOB da kuma sojin Najeriya abin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiya.