Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kun san me ya janyo yakin Biafra?
Latsa alamar lasifika domin sauraren hirar Ibrahim Isa da Alhaji Tanko Yakasai
Najeriya za ta cika shekara hamsin da kawo karshen yakin basasar da aka yi a kasar, wanda ya yi sanadin asarar dimbin rayukan jama'a da dukiya.
Shekara uku aka shafe ana yakin, wanda al'umar kudu masu gabashin kasar suka yi yunkurin ballewa domin su kafa tasu kasar mai suna Biafra, karkashin jagorantin Kanar Odumegu Ojukwu.
Alhaji Tanko Yakasai dattijon da ya san zamanin da aka yi yakin, ya yi wa Ibrahim Isa bayani kan abin da ya haddasa yakin basasar: