George Floyd: 'Annobar wariyar launin fata ce ta yi sanadin kashe' baƙar fatar

Wani lauyan George Floyd, bakar fatar da 'yan sanda suka kashe a birnin Minneapolis na Amurka, ya shaida wa taron jana'izar marigayin cewa "annobar wariyar launin fata ce ta yi sanadin kashe shi."

Mutanen da suka halarci jana'izar sun yi tsit na minti takwas da dakika 46, wato adadin lokacin da Mr Floyd ya shafe a kwance a kasa lokacin da wani dan sanda ya sa gwiwarsa ya danne wuyansa har ya mutu.

Daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar tasa, wacce fitaccen mai fafutukar kare hakkin dan adam din nan na Amurka, Rebarand Al Sharpton, ya yi wa jawabi.

A cewarsa, lokaci ya yi da za a tashi tsaye sannan a ce "wannan rashin mutunci ya isa".

Kisan da aka yi wa Mr Floyd, wanda aka nada a bidiyo, ya janyo tarzoma a fadin Amurka da ma wasu kasashen duniya.

Sai dai a yayin da ake yi masa jana'iza, a waje guda an gurfanar da wasu 'yan sanda uku a gaban kuliya bisa zarginsu da hannu a wajen kisan nasa.

An bayar da belinsu a kan $1m ko da yake za a rage zuwa $750,000 idan suka mika bindigoginsu da kuma cika wasu sharuda, a cewar alkalin da ke yi musu shari'a.

An zargi Derek Chauvin, dan sandan da ya danne wuyan Mr Floyd lokacin da ya rika cewa ba ya iya numfashi, da kisan kai kuma zai gurfana a gaban kuliya ranar Litinin.

Gabilin wadanda suka kwashe kwana takwas suna zanga-zanga kan kisan Mr Floyd, sun yi ta ne ciki lumana, ko da yake wasu sun ria tayar da tarzoma da fashe-fashen wurare da sata, lamarin da ya sa aka sanya dokar hana fita a wasu biranen Amurka.

Mene ne ya faru lokacin jana'izarsa?

Da yake jawabi ga mahalarta janai'izar Mr Floyd, lauyansa Benjamin Crump ya ce ba "annobar korona ce ta yi ajalin George Floyd ba".

"Annobar wariyar launi fata ce ta kashe shi," in ji shi.

Iyalan Mr Floyd, da Rebarand Jesse Jackson, da gwamnan MinnesotaTim Walz, da dan majalisar dattawan jihar ta Minnesota Sanata Amy Klobuchar da kuma Magajin birnin Minneapolis Jacob Frey suna cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana'izar tasa a North Central University da ke Minneapolis.

Philonise Floyd, daya daga cikin 'yan uwan Mr Floyd, ya bayyana yadda mahaifansu suke fama da talauci lokacin da shi da Mr Floyd suke kananan yara da kuma yadda suke wanke tufafinsu a bahon karfe sannan su shanya su a ciki na'urar dumama abinci.

"Wannan abin al'ajabi ne, dukkan wadannan mutanen sun zo nan ne domin ganin dan uwana, wannan abin alfahari ne wanda ya ratsa zuciyar mutane da dama," a cewarsa.

A nasa bangaren, Rebarand Al Sharpton ya bukaci hukumomi su yi adalci kan kisan Mr Floyd.

"Ba za mu dakata ba," a cewarsa, yana bayani ne a kan zanga-zangar da ta mamaye biranen Amurka. "Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai an samu sauyi game da tsarin shari'ar kasar nan."