Coronavirus a Najeriya: Mutum 260 sun sake kamuwa, 12 sun mutu

Covid-19

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jihar Abia da babban birnin ƙasar Abuja sun ture Legas daga matakin gaba na yawan masu cutar a ranar Lahadi
Lokacin karatu: Minti 3

Mutum 260 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya, kamar yadda alƙaluman hukumar daƙile cutuka ta ƙasar suka nuna. Jimillar masu cutar yanzu ya kusa 12,500.

Sabbin alƙaluman hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa sun nuna samun raguwar mutanen da suka kamu a Legas, jihar da annobar ta fi ƙamari. Mutum 38 ne suka sake kamuwa cikin sa'a 24.

Kuma karon farko ke nan da aka samu wata jiha da ta fi Lagos yawan mutanen da suka kamu da annobar kwana 100 da zuwanta Najeriya.

Alƙaluman na hukumar NCDC a daren Lahadi sun nuna cewa jihar Abia, ita ce a kan gaba da yawan mutanen da suka sake kamuwa da korona. Sabbin masu cutar 67 aka gano a jihar ta Abia.

Haka kuma, a Abuja an sake gano mutum 40 da wannan cuta. A baya-bayan nan dai, yawan masu cutar ya ƙaru a babban birnin na Najeriya.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Alƙaluman na daren Lahadi sun kuma nuna cewa cutar ta sake yin ajalin mutum 12 cikin sa'a 24 a Najeriya. Yawan mutanen da suka mutu a faɗin ƙasar saboda annobar 354.

Duk da haka, NCDC ta ce an sallami mutum 133 da aka tabbatar sun warke a Lahadin nan. Adadin mutanen da suka warke daga korona ya doshi 4,000.

Wannan na zuwa ne yayin da aka tabbatar mutum 19 sun sake harbuwa da cutar a jihar Ogun. Sai Gombe, inda aka samu adadin sabbin masu cutar 16. Yawan masu cutar a Gombe 217 yanzu.

Jihar Edo mutum 14 ne aka ba da rahoton sun sake kamuwa, sai Imo mai mutum tara.

Jihohin Katsina da Kwara da Nasarawa da Borno, an sake gano sabbin masu cutar takwas-takwas. Yawan masu korona a Katsina, 400 ba biyar.

Mutum shida sun sake harbuwa a Kaduna. Sai mutum biyar daga Bauchi. Ekiti na da sabbin masu cutar huɗu.

Jihohin Kano da Neja da Filato da Sokoto da Ekiti, an gano mutum bibbiyu sun sake kamuwa a cikin kowaccensu.

A makon jiya ne, gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta sallami duk masu jinyar da suka rage a cibiyar killacewarta bayan an tabbatar da warkewarsu kafin daga bisani a ranar Asabar, a sake gano wasu da suka kamu.

@NCDCgov

Asalin hoton, @NCDCgov

Bayanan hoto, Tun bayan ɓarkewar annobar korona, Najeriya ta yi ƙoƙarin ƙara yawan cibiyoyin gwaje-gwaje da horas da jami'an lafiya

Muhimman bayanai kan annobar korona

A wani abu da ba a taɓa gani ba tun bayan ɓullar korona Najeriya, hukumomin ƙasar ranar Asabar 30 ga watan Mayu, sun ba da rahoton gano mutum 553 da cutar ta sake harba.

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.

Jiha ɗaya ce ta rage yanzu a Najeriya cutar ba ta bulla cikinta ba wato jihar Cross Rivres. Wasu dai na zargin cewa mai yiwuwa annobar ta shiga jihar, rashin yin gwaji ne ya sa aka ba a iya gano ta ba.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji fiye da dubu ɗaya cikin sa'a 24.

@NCDCGOV

Asalin hoton, @NCDCGOV

Bayanan hoto, Hukumar NCDC ta ce Najeriya na haɓaka ƙoƙarinta wajen wayar da kai da faɗakar da al'umma a unguwanni da yankuna

Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Asabar 6 ga watan Yuni.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X