'Sojojin Jamhuriyar Nijar ne suke ba mu tsaro ba na Najeriya ba'

Asalin hoton, Website/Gobir
Majalisar dattijai a Najeriya ta tabka muhawara kan matsalar tsaro da ta addabi yankunan arewacin kasar inda ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya faɗaɗa umurnin da ya ba sojojin kasar na fatattakar barayi a jihar Katsina zuwa sauran jihohin da 'yan fashin suka addaba wato Zamfara da Kaduna da Niger da kuma Sokoto.
Sanata Sabi ya'u na jihar Neja ne ya gabatar da bukatar, inda Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya mara wa bukatar baya kuma majalisar ta amince.
Wasu 'yan majalisar daga jihohin sun ce barayin za su gudu ne daga Katsina su koma domin fakewa a jihohinsu.
Daya daga cikin 'yan majalisar daga Sokoto na Jam'iyyar APC ya zargi sojojin Najeriya da gazawa tare da cewa yanzu sun dogara ne ga sojojn Nijar.
Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya ce "babu ranar da ba a kai mana hari. Ko dai a sace mana dabbobi ko a cinye maka amfanin gona.
Babu mai kai mana dauki. Har ma sojojin jamhuriyar Nijer domin idan ka kira na Najeriya sai dai su je su yi tsaye ba sa iya komai.
To sai dai mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya ce korafin 'yan majalisar ya zo a kan gaba kasancewar akwai shirin da rundunar sojin Najeriya ke shiriyawa a yankunan mai suna "Operation Accord".
Wata kungiyar mai sa ido kan rikice-rikice International Crisis Group ta ce an kashe mutum fiye da 8000 sannan fiye 200,000 sun bar muhallansu sakamakon tashe-tashen hankali da hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya a cikin shekaru 10.
Ko da a ranar Litinin ma rahoatnni sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari wasu kauyuka a karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutum 10.











