Coronavirus a Najeriya: Me ya sa gwamnoni ke shan bamban da Buhari?

Damuwar da fadar shugaban Najeriya ta nuna game da yadda wasu gwamnonin jihohin suke yin gaban kansu a yaki da cutar korona ta jefa alamar tambaya kan yadda ake yaki da cutar.

A tattaunawarsa da BBC, Malam Garba Shehu, mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin watsa labarai ya ce abin takaici ne a ce gwamnatin tarayya tana daukar matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai daga gwamnonin jihohi.

Ya ce ''ba wai zargi muke yi ba ko kushe, amma akwai bukatar a ce ana tafiya tare saboda idan matsaya ba ta zo guda ba, da wuya a yi nasara a yaki da korona''.

Malam Garba Shehu, ya ce kwamitin da ke yaki da annobar na kasa na kokawa kan yadda matakan wasu jihohi ke warware nasarorin da ake samu akan annobar.

"Kamata ya yi kafin a dauki kowanne irin mataki, to a tuntubi masana domin neman shawarwari," in ji mai magana da yawun shugaba kasar.

Ko da yake kakakin na Buhari bai fito karara ya ambaci sunan wani gwamna ba, amma masana harkokin yau da kullum suna ganin yana shagube ne a kan matakan da wasu gwamnoni irin su Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Gwamna Aminu Bello Masari da Gwamna Dapo Abiodun da Gwamna Nasir El-Rufai da ma wasunsu da dama kowanne yake yin gaban kansa a yaki da cutar ta korona.

Misali, duk da umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na sanya dokar kulle ta mako biyu a jihar Kano lokacin jawabin da ya yi wa 'yan kasar saboda karin mace-macen da ake samu a jihar wadanda wasu suke dangantawa da cutar korona, amma Gwamna Ganduje ya sanar da sassauta dokar.

Gwamnatin Kano ta ce mazauna birnin Kano za su iya fita a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma domin sayen abinci da magani, lamarin da masana harkokin lafiya, irin su Farfesa Usman Yusuf, tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya kuma kwararren likita ke gani tamkar yin tufka da warwara ne.

Kazalika, Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, inda a nan aka samu likitan farko da ya mutu sanadin cutar ta korona, yayin da cutar take ci gaba da adda'ar jihar, ya ce zai bari a gudanar da Sallar Idi, abin da masana harkokin lafiya suke ganin zai sa a samu sabbin mutane da za su kamu da cutar.

A nasa bangaren, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya dauki matakin barin mazauna jihar su rika fita a ranakun Laraba da Juma'a tsakanin karfe bakwai na safe zuwa karfe biyar na yamma, duk da yake jihar na cikin jihohin da suka fi fama da cutar korona.

Shi kuwa Gwamna Nasir El-Rufai, ya rufe dukkan hanyoyin da za a shiga jihar Kaduna, sannan ya sanya dokar kulle ta wata guda, yanzu kuma ya ce ba za a gudanar da Sallar Idi ba.

Ko da yake masana kiwon lafiya na cewa da ma ya kamata kowacce jiha ta duba irin matakan da suka dace da ita wajen yaki da cutar, amma wasu masanan na ganin tun farko gwamnatin tarayya ce bata dauki matakin da ya dace na baidaya a fadin kasar ba, shi ya sa kowanne gwamna yake yin abin da yake ganin zai fisshe shi a yaki da cutar korona.

Bayar da kafa ta faruwar hakan

A gefe guda kuma, wasu masu sharhi, irin su Ahmad Yahuza Getso, na ganin tsarin mulkin federaliya da Najeriya take bi shi ne ya bai wa gwamnonin damar daukar matakan da gwamnatin tarayyar ke kokawa a kai.

"Gwamnatin tarayya ita ta fara bayar da kafa ta faruwar hakan. Da suka tara gudunmawa [na yaƙi da cutar] sai da suka yi wajen sati hudu basu ce wa gwamnoni komai ba. Sannan ba su sa ido a kan kudaden da su kansu gwamnoni suka tara ba, kuma ga matsin lamba da gwamnonin suke samu daga malamai da kungiyoyi masu zaman kansu da mutanen da suka san ciwon kansu, da kuma mu masana tsaro, wadanda suka san illa da hatsarin kulle mutane a gidaje ba tare da an yi tanajin abin da ya kamata ba" in ji Ahmad Getso

Masu lura da lamura dai suna ganin wannan zaman 'yan marina da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi game da yaki da cutar korona kaniya rikidewa ya zama takaddamar siyasa da kuma batun hurumi a fuskar doka. Duk wannan kuma ka iya kawo cikas a yaki da cutar ta korona wadda ke ci gaba da yin barna a kasar.

Sai dai sun ce za a iya kauce wa hatsarin sabanin muddin gwamnatoci a matakan biyu suka zauna suka fahimci juna sannan suka dauki matakan da suka dace; ko da kuwa matakan ba za su yi wa wasu dadi ba, matsawar dai za su iya dakile cutar.