Yadda China ta sauya rayuwar wasu mutanen ƙauye da ke kan tsauni

People climb on the newly-built metal ladder with hand railings to Ahtuler village on a cliff on November 11, 2016

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Labarin kauyen ya yadu sosai bayan da aka nuna hotunan mutanen goye da jariransu suna hawa tsani don zuwa gidajensu.

China ta sauko da wasu mutane da ke zaune kuma suke rayuwa a wani tsauni mai tsawon mita 800, a wani shiri na yaki da talauci.

A baya mutanen suna daukar tsaunin a matsayin gida, amma yanzu an sake wa dubban mazauna kauyen da ke Lardin Sichuan matsuguni zuwa wasu rukunan gidaje a birni.

Kauyan na Atulie'er dai ya yi suna a duniya, bayan bayyanar hotunan manya da yara da ke amfani da tsani wajen hawa tsaunin.Magidanta kusan 84 ne tare da iyalansu suka ci gajiyar wannan gagarumin shiri na gwamnatin China na yaki da talauci a fadin kasar zuwa karshen 2020.

Hukumomin sun sauko da mutanen da ke zaune a wannan kauye nasu da ke kan tsauni, wanda hawansa kadai ba ma tare da abubuwan bukatunsu ba abu ne mai hadarin gaske, amma a wurinsu abu ne da ya zama jiki saboda ba su da zabin da ya fi hakan, kuma su a wurinsu ba wata kasada ba ce.

Kauyen Atulie'er da ken kan dogon tsauni ya dauki hankalin hukumomin kasar ta China da ma duniya bayan da a shekara ta 2016 aka bayar da rahoton al'ummar da yadda suke rayuwarsu ta irin yadda suke amfani da wani tsani ko kuranga ta igiya su hau tsaunin su je gidajensu da kayansu na masarufi, wani lokaci ma matansu goye da jarirai.

Bayan bayyanar wannan labari nasu, sai nan da nan gwamnatin China ta kai musu dauki, inda ta musanya musu tsanin da suke amfani da shi, na katako da wani na musamman na karfe, mai saukin hawa ba tare da wani hadari ba.

Bayan wannan dauki ne kuma sai hukumomin kasar suka shiga tsarin yadda za su sauko da mutanen daga wannan tsauni ma gaba daya, a raba su da wannan rayuwa, inda a yanzu bayan kammala wasu rukunan gidaje, a garin da ke nisan kilomita 70 daga tsaunin da suke.

Gwamnatin ta gina rukunin gidajen ne a karkashin shirinta na yaki da talauci inda ta ba kowanne magidanci da iyalansa gida daidai da yawan iyalansa a farashi mai sauki da zai mallake shi.

The new apartment blocks

Asalin hoton, CGTN/Youtube

Bayanan hoto, Mutanen za su rika rayuwa a wannan rukunin gidajen

Wani magidanci da ya amfana da shirin ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda rayuwa ta sauya masa a yanzu, da cewa yana farin ciki da a yayu ya samu gida mai kyau da zai zauna da shi da iyalansa.

Sai dai kuma kusan magidanta 30 za su ci gaba da zama a wannan kauye nasu na Atulie'er da ke kan tsauni, amma kuma da wata sabuwar rayuwa ba kamar ta da ba.

Domin hukumomin kasar ta China za su mayar da kauyen ne ya zama wani wuri na yawon buda idanu, inda su wadannan magidantan za su rika aikin tafiyar da harkokin buda idanun wajen gudanar da gidaje ko dakuna da wuraren cin abinci na masu zuwa yawon buda idanu, da kewayawa da su.

Haka kuma a burin hukumomin yankin na raya kauyen da bunkasa harkar za su sanya irin 'yar karamar motar nan da ke tafiya a sama da kugiya domin hawa da 'yan yawon buda idanu da kuma raya sauran yankunan da ke makwabtaka da kauyen.

Villagers Living On Cliff Shop Online In Liangshan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, his is the journey the villagers had to make to get home