Coronavirus: Atiku ya shawarci Buhari ya sayar da jiragen shugaban ƙasa

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Atiku Abubakar ya ce har yanzu gwamnatin Najeriya bata san mawuyacin halin da cutar korona ta jefa duniya ciki ba
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya shawarci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sayar da jiragen da ke fadarsa domin a samu karin kudin tafiyar da harkokin kasa.

Atiku Abubakar ya bayar da shawarar ce sakamakon matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na rage kasafin kudin kasar saboda faduwar farashin man fetur a duniya.

Najeriya ta kiyasta kasafin kudin na 2020 ne bisa $57 a kan kowacce gangar mai daya amma annobar korona ta sa farashi ya yi muguwar faduwa a duniya, lamari da ya sa kasar ta rage kiyasin zuwa $30 kan gangar mai daya kuma hakan zai shafi kasafin kudinta na bana.

Sai dai a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce "abin mamaki ne a gare ganin cewa duk da faduwar farashin man fetur, da kuma gazawar Najeriya wajen kara samun kudin shiga daga bangarorin da ba man fetur ba, gwamnatin Najeriya ta yi ragi kadan na kasafin kudinta da kashi 0.6. Hakan na nufin an rage ₦71 bn kawai."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ya kara da cewa hakan ya nuna cewa har yanzu Najeriya bata san mawuyacin halin da duniya take ciki ba.

"Ya kamata a rage kasafin kudi mai matukar yawa na fadar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya. Dole a soke kasafin kudin da aka yi na saya wa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da sauran masu rike da mukaman siyasa motocin alfarma.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

"Kada a taba albashin ma'aikata, amma a rage albashin masu rike da mukaman siyasa. A sayar da jirage 8 ko 9 da shugaban kasa yake amfani da su", in ji Atiku.

A cewarsa, ya kamata a soke kasafin kudin da aka yi wa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa don yin tafiye-tafiye.

"Haka kuma ya kamata a soke kasafin kudin ₦27 bn da aka yi da zummar gyara majalisar dokoki", a cewar tsohon mataimakin shugaban Najeiya.

Ya kara da cewa bai kamata a rage kasafin kudi da kasa da kashi 25 cikin dari ba domin kuwa 'yan Najeriya ba za su so hakan ba.