Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Ko China tana iya yi wa duka mutanen Wuhan gwaji cikin kwana 10?
- Marubuci, Daga Pablo Uchoa da Vincent Ni
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana shirin China na yaki da cutar korona a matsayin mafi girma a tarihi.
Amma burin kasar na gwada duk mutanen birnin Wuhan cikin kwana goma ya jawo ce-ce-ku-ce.
Hukumomin kasar sun shirya yadda za su gwada mutum miliyan 11 da ke birnin, inda za a fara da mutanen da ke cikin hatsarin kamuwa da cutar korona da kuma ma'aikatan lafiya.
Gwaje-gwajen za su nuna idan har yanzu akwai masu dauke da cutar ta covid-19, ko a'a.
Amma wannan na nufin birnin Wuhan zai gwada a kalla mutum miliyan 1 na mazaunansa kowacce rana - kuma a halin yanzu mutum 40,000 zuwa 60,000 ake iya gwadawa a kullum.
"Muna sa ran ganin abin da ba a taba gani ba," in ji Yanzhong Huang, wani jami'i a cibiyar lafiya da ke birnin New York na Amurka.
Me ya sa ake son gwada mutane da yawa?
An sanar da wannan shirin ne bayan gano mutum shida dauke da cutar korona cikin wata unguwa da ke birnin na Wuhan a karshen mako.
A baya an ce mutanen na dauke da cutar amma ba sa nuna wasu alamomi nata - kamar tari da mura.
Bayan wannan ne, aka umarci dukkan mutanen unguwar kimanin 5,000 su yi gwaji.
Wasu na ganin cewa cikin mazauna birnin Wuhan miliyan 11 da suka yi rajista, wasu sun yi balaguro kafin dokar kulle ko kuma an yi masu gwajin ba da dadewa ba.
Don haka, hukumomi ba za su ji jiki ba idan suka fara aikin gwajin na kwana 10.
An riga an yi wa mazauna Wuhan tsakanin miliyan uku da miliyan biyar gwaji, Yang Zhangiu, mataimakin shugaban sashen gwaji na Jami'ar Wuhan ya shaida wa jaridar Global Times.
"Wuhan na iya gwada sauran mutum miliyan shida zuwa takwas a kwana 10," a cewarsa.
Amma ko da an rage yawan mutanen da za a yi wa gwajin zuwa miliyan shida ko takwas, wannan na nufin kowacce rana sai an gwada mutum 600,000 ko 800,000 idan hukumomin sun dage lallai a kwana 10 za su kammala aikin.
Wannan kalubale ne. Ranar 22 ga watan Afrilu, gwamnatin lardin Hubei ta ruwaito cewa ana yi wa mutum 89,000 gwaji a kullum.
Ta kara da cewa a Wuhan, babban birnin lardin na Hubai, yawan mutanen da ake gwadawa kullum ya kai 63,000.
Sannan ranar 10 ga watan Mayu, hukumomi sun ce an yi gwaji kasa da 40,000 a Wuhan a rana guda.
Yaya za a yi wa miliyoyin mutane gwaji cikin kankanen lokaci?
Wasu na ganin cewa idan hukumomin China da gaske suke, za su iya cimma burinsu.
Ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, kafar yada labarai ta China Caixin ta ruwaito hukumar dakile cutuka masu yaduwa a China na cewa ana yi gwaje-gwaje da yawa ne ta hanyar amfani da wasu kamfanoni.
Hukumomin CDC na yankuna da asibitoci a fadin birnin za su tura ma'aikatansu su je don yi gwajin.
Jami'in ya yi kiyasin cewa kamfanonin da ke yin aikin na iya yin gwaji 100,000 a rana, kuma ya ce zai yi wuya a iya yin gwaji da yawa cikin dan kankanen lokaci.
"Don haka, za a rarraba aikin, wato za a fara yi wa wasu yankunan birnin daga 12 ga watan Mayu: wasu kuma daga 17 ga watan Mayu, misali. Kowane yanki zai gama gwajinsa cikin kwana goma daga ranar da aka fara yi masa."
China na iya samar da kayan gwaji miliyan 5 a rana, a cewar ma'aikatar masana'antu ta kasar. Kuma ana ci gaba da gina cibiyoyi da dakunan gwaji.
Wasu, ciki har da farfesa Yang sun ce babu dalilin gwada dukkan mazaunan Wuhan idan babu mai dauke da cutar a unguwa.
"Ba za ka taba sani ba idan mutane ba sa dauke da cutar […] Kawai dai ana so ne a yi bincike don gane ainihin halin da ake ciki," ya shaida wa jaridar The Global Times.
'Tsoron sake barkewar annoba'
Yayin da kasashe da dama ke sassauta dokar kulle, hukumomi na fargabar sake barkewar annobar.
Wuhan ta sassauta dokar kullen ta tsawon mako 11 ranar 8 ga Afrilu amma ana fargabar sake barkewar korona bayan mutanen da aka gano kwanan nan dauke da cutar.
Ana daukar matakan kariya a wasu wuraren na China: a birnin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar misali an killace shi daga sauran yankunan kasar.
Kuma mazaunan da aka gwada aka tabbatar ba sa dauke da cutar ne kawai ake bari su bar garin.
An dakatar da motocin haya da jiragen kasa da silima da wuraren motsa jiki daga aiki.
Wu Zunyou, babban jami'I a Hukumar Dakile Yaduwar Cutuka ya ce gwamnati ta zage damtse ko da za a sake samun masu cutar bayan sun warke.
"Wato akwai fiye da irin wannan a Wuhan: cutar na yin kwana 30 zuwa 50 a jikin wasu marasa lafiya," in ji Wu.
"Kwayar cutar na iya dadewa ba ta bayyana ba a mutanen da garkuwar jikinsu ba ta da karfi, kuma alamomin cutar kan bayyana sama-sama a tare da su."
Wu ya kara da cewa "ba dole ne" a gwada kowa ba a Wuhan musamman cikin unguwannin da ba a samu mai dauke da cutar ba.
Gwajin zai yi 'matukar tsada'
Gwada dukkan mutanen da ke Wuhan zai yi "matukar tsada", in ji farfesa Huang.
"Amma ku tuna fa China ce wannan. Yadda suka kaddamar da kullen nan, tsauraran matakan da suka dauka - duk suna da matukar tsada.
"Amma wannan shi ne fatan da ma: ko nawa za a kashe, a tabbatar da kariya."
Matakan da China ta dauka kan cutar korona sun sha bamban sosai da na sauran kasashe.
A Amurka, ana gwada mutum 300,000 a rana kuma Shugaba Donald Trump na shan suka saboda rashin jaddada dokokin ba da tazara, duk da yake kasarsa ce ta fi kowacce yawan mutanen da korona ta kashe.
Hukumomin China na ganin cewa, wannan ya nuna yadda tsarin China ya yi wa na Amurka fintinkau, a cewar Farfesa Huang.
Amma kuma tsarin na yanzu ba zai magance matsalar sake barkewar cutar ba nan gaba, a cewarsa, saboda gwajin zai nuna masu dauke da cutar ne kawai a yanzu.
"Akwai yiwuwar nan gaba za a iya sake samun bullarta, abin da gwajin mutane masu yawa a lokaci guda ba zai dakatar ba," ya ce.
Yitsing Wang a Beijing ya taimaka wajen hada wannan rahoton.