Faduwar farashin man fetur da yakin Yemen na gigita Saudiyya

Ba a dade ba da 'yan Saudiyya suka rika rayuwar da ba sa biyan haraji, amma sai ga shi kasar ta ninka harajin VAT daga kashi 5 cikin 100 zuwa kashi 15 cikin 100, sannan daga watan gobe ta kuma soke tallafin rayuwa da take bai wa 'yan kasar.

Wadannan matakan na zuwa ne a daidai lokacin da farshin danyen man fetur a kasuwannin duniya ya fadi kasa warwas, matakin da ya zaftare kudaden shigar Saudiyya da kashi 22 cikin 100.

Kamfanin man fetur na Saudiyya Aramco kuma ya yi asarar kashi daya cikin hudu na ribar da ya sa ran samu a watanni uku na farkon shekarar nan.

A halin da ake ciki, annobar Covid-19 na yiwa tattalin arzikin Saudiyya mummunan ta'adi. Tatalin arzikin da ya dogara kan miliyoyin ma'aikata daga yankin Asiya da ke rayuwar kunci a muhallai mara tsafta.

Yakin da kasar ke yi a Yemen ya sanya ta tafka asarar kudaden da ya kamata a rika gina kasa da su.

Amma duk da haka kasar na da abin tunkaho da ka iya rufa mata asiri - Akwai Saudi Aramco - kamfanin mai na kasar da darajarsa ta kai dala tiriliyyan 1 da biliyan 700.

Kamfanin dai ya shafe darajar Google da Amazon baki dayansu. Amma duk da haka akwai damuwa ganin irin halin da Saudiyya ta samu kanta a yau.

A watanni uku na bana, kasar ta sanar da wani wageggen gibi na dala biliyan 9 da take bukata domin aiwatar da kasafin kudinta na wannan shekarar.

Cutar korona kuma ta yi fatali da dukkan manyan ayyukan gina kasa a fadin kasar, wanda ka iya hana ta cimma wani shiri da Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya dora kasar kan tafarki na samar da wasu hanyoyin kudin shiga.

A fagen dangantakar diflomasiyya kuwa, Saudiyya ba ta ga maciji da makwabtanta Iran da Kuwait, sannan yakin da ta ke yi da 'yan Houthin Yemen ya janyo ma ta suka saboda asarar rayukan da wahalhalun da ya haifar.

Sannan a bana da wuya kasar ta sami wasu kudaden shiga na a zo a gani daga aikin Hajji saboda cutar korona.

Ba sai an fada ba, amma Saudiyya na tsaka mai wuya.