Yadda aka yi girgizar kasa a yankin Makkah na Saudiyya

An samu girgizar kasa mai karfin maki 2.7 a gabashin Qunfudah da ke cikin yankin Makkah kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.

An samu girgizar kasar ne ranar Alhamis jajibirin azumin Ramadan. Kuma hukumomin Saudiyya sun ce duk da girgizar kasar ba ta yi karfi ba, amma mutanen yankin sun ji girgizar.

Hukumomi sun ce ba wannan ne karon farko da aka taba samun girgizar kasa a yankin ba, kuma ba su da karfin da tasirinsu zai haifar da wani ta'adi ga al'umma.

Saudiyya ta ce tana daukar matakai tare da yin kira ga al'ummar kasar cewa lamarin ba wani abin tsoro ba ne ko haifar da fargaba.

Karin labaran da za ku so ku karanta