Coronavirus: Mutum 471 sun mutu a jihar Yobe a ƙasa da wata guda

Mutum 471 sun mutu a jihar Yobe cikin mako uku, kamar yadda kwamitin kar-ta-kwanan yaki da cutar korona ya bayyana ranar Talata.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin kan yaki da cutar, ya ce mafi yawan wadanda suka mutun dattijai ne.

Ya kara da cewa dukkansu mutanen sun mutu ne tsakanin makon karshe na watan Afirilu da kuma makonni biyun farko na watan Mayu.

Kamar yadda kwamishinan ya fada, an fi samun mace-macen a Potiskum wanda shi ne cibiyar kasuwancin jihar da Nguru da Gashuwa da kuma Damaturu in da nan ne babban birnin jihar.

Kamar dai sauran jihohin arewacin kasar da suka hadar da Bauchi da Borno da Jiugawa da kuma Kano, ana ta nuna damuwa kan karuwar mace-mace da ke da alaka da cutuka daban-daban a Yobe.

Amma ma'aikatan lafiya da masu hasashe na da ra'ayin cewa mace-macen da aka samu a makonnin da suka gabata a yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso gabashi, na da alaka da cutar korona.

Sai dai hukumomi na alakanta wannan mace-macen da sauran cutuka da aka manta da su, kamar su zazzabin cizon sauro da matsanancin zafi da ake fama da shi da hawan jini da ke damun manyan mutanen watakila kuma da annobar korona.

An ruwaito cewa sama da mutum 200 sun mutu a Kano, a Jigawa da Bauchi ma sama da 300 sun mutu a makonnin bayan.