Coronavirus: 'Ƙananan yara kusan 1000 ka iya mutuwa a kullum a Najeriya'

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar yara 'yan kasa da shekara biyar fiye da 950 za su iya mutuwa a kullum a Najeriya sakamakon yadda cutar coronavirus ke kawo cikas da kuma kokarin gurgunta bangaren kiwon lafiya.

Asusun ya bayyana cewa za a iya samun irin wadannan mace-mace a kasar muddun ba a dauki matakai na gaggawa ba.

A wani bincike da jami'ar Johns Hopkins ta gudanar, ya nuna cewa kusan yara 6,000 za su iya mutuwa a kullum a fadin duniya.

An bayyana cewa kuma za a iya samun mutuwa wajen haihuwa na kusan mutum 6,800 a Najeriya a watanni shida masu zuwa.

A Najeriya, wadannan mace-macen yaran za suj zama kari ne ga yara 475,000 da suke mutuwa kafin cika shekaru biyar a duk bayan watanni shida - wanda hakan zai mayar da hannun agogo baya a yunkurin da ake yi na shawo kan matsalolin mace-macen kananan yara a kasar.

Kamar yadda binciken ya nuna, kasashen da ke kan gaba wadanda ake sa ran kananan yara za su fi mutuwa idan ba a dauki mataki ba su ne Bangladesh da Brazil da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo da Ethiopia da Indiya da Indonesia da Najeriya.

Sauran kasashen sun hada da Pakistan da Uganda sai kuma Tanzania.