Mace-macen Kano: Aikin da kwararrun likitocin Abuja za su yi a Kano

Wani ayarin kwararrun likitoci ya shiga Kano da ke arewacin Najeriya daga Abuja, cibiyar gwamnatin tarayya don taimaka wa jihar game da ta samu kanta.

Yawan mace-macen da ake samu a kusan daukacin unguwannin birnin Kano ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummar jihar da ma takwarorinsu a fadin kasar musamman na arewaci.

Kano dai ita ce babbar cibiyar kasuwanci tsakanin jihohin arewa da ma wani bangare na yankin Afirka ta Yaamma, kuma dumbin mutane ne daga fadin Najeriya suke shiga suna fita kullum don harkokin ciniki.

Dakta Sani Gwarzo shi ne shugaban ayarin likitocin gwamnatin tarayyar zuwa Kano, ya kuma shaida wa BBC cewa ayarin nasu ya kunshi kwararrun likitoci da dama kuma sun je ne don taimaka wa jihar wajen shawo kan matsalolin da take fuskanta da kuma dakile yaduwar korona.

Ana samun mace-mace babu kakkautawa cikin 'yan kwanakin nan a Kano, kuma ko a karshen makon nan an fuskanci mutuwar wasu manyan mutane, kama daga malaman makaranta da 'yan kasuwa da ma sauran 'yan garin da ba a kai ga jin duriyar tasu mutuwar ba.

Rashin sanin musabbabin mace-macen shi ne ya fi daga wa al'umma hankali, lokacin da ake tsaka da fama da annobar korona.

Makasudin aika tawagar

Dakta Sani Gwarzo ya ce "binciken gawawwakin da ke mutuwa babu gaira babu dalili, don tabbatar da ko wadannan mace-mace na da alaka da annobar korona? ko kuma ta fi alaka da zazzabin Lassa wanda jihar ta yi fama da shi a baya?

Jin ra'ayoyin masana da kuma daidaikun mutane har da gwamnati don sanin me ake yi zuwa yanzu saboda a dakatar da wannan annoba (na daga cikin abubuwan da muka sanya gaba).

Tattara bayanai da kuma samar da kayan aiki wadanda za a dukufa wajen tunkarar wannan cuta da su don ganin mutuwar da ake fama da ita ta ragu."

Ya kara da cewa a lokacin da ake kokarin shawo kan yawan mutuwar da ake samu, ana kuma yaki da cutar korona a lokaci guda.

Mutanen da ke cikin ayarin

Cikin likitocin akwai: Farfesa Abdussalam Nasidi tsohon babban daraktan farko a hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC, wanda sanannen likita ne da ke da ilimi kan abubuwan da suka shafi kwayoyin cuta, ciki har da abin da ya danganci Ebola da Lassa da saurarnsu.

Akwai shugabar asibitoci ta ma'aikatar lafiya ta kasa, Dakta Bimpe Adebiyi.

Dakta Sa'id Amin, masani ne kan al'amuran da suka shafi mutuwa da gawa da kuma musabbabin mutuwa shi ma yana cikin ayarin.

Akwai kuma rukunin likitoci masu ilmin cutuka masu yaduwa da ke bin diddigin yadda cuta ke bazuwa kamar mutum uku a cikin tafiyar.

Sun tafi da masana daga bangarori guda uku, akwai kwararriyar ma'aikaciyar jinya da aka je da ita daga cibiyar yaki da 'yan kananan kwayoyin cutuka ta Irrua a Jihar Edo.

Akwai wakilcin gwamnatin jihar Legas da kuma jami'ai daga cibiyar bincike ta Najeriya da ke jihar ta Legas.

Wadannan kadan ne daga cikin mutanen da ke cikin wannan tafiya kuma su ne za a fara aikin da su.

Dakta Sani Gwarzo ya ce "An ba mu damar duk wanda muka ga zai iya taimaka wa cikin wannan tafiya, za mu iya hada hannu da shi domin kai wa ga nasara."

Ya ce ya zuwa yanzu ba su kayyade kwana nawa za su yi (a Kano) ba, amma da zuwansu, sun ziyarci a kalla wuri bakwai, "don haka aiki ne za a yi ba dare ba rana sai an cimma gaci," in ji shi.

Matsalolin da aka gano

Duk da yake an tanadi asibitoci da gadaje amma babbar matsalar da ake fuskanta a Kano ita ce aikin gwada mutanen da ake zargi sun kamu da korona ya tsaya cak, cibiyar da aka ware don wannan aiki ta samu matsala tsawon kwanaki.

Sai dai mahukuntan sun ce ya zuwa ranar Talata komai ya daidaita kuma cibiyar ta sake budewa don ci gaba da aikin gwaje-gwaje.

Duk da an samu gudunmawar wata karamar cibiya da kuma kayan aiki daga Jami'ar Bayero Kano amma ita ma ba ta fara aiki ba, sai nan da 'yan kwanaki.

Kuma duk wani mataki da za a iya dauka domin dakile wannan matsaloli ya ta'allaka ne a kan gwajin cutuka da za a yi wa al'umma, don tantance hakikanin larurorin da suke fama da su.

Akwai matsalar da ke kara dagula wannan hali da kano ke ciki, in ji Dakta Gwarzo, " Yadda ake mantawa da masu kananan cutuka ko kuma cutukan yau da kullum da ake fama da su, kama daga hawan jini da irinsu ciwon kai da sauransu."

A iya cewa aikin shawo kan korona ya jefa masu kananan larurori cikin halin ni-'ya-su da garari a asibitocin Kano.

Wadannan matakai na zuwa ne bayan a jawanbin shugaban kasar Muhammadu Buhari a daren Litinin, ya ce zai aika ayarin likitoci zuwa Kano don kai dauki da gudanar da bincike.

Shugaban ya kuma sanar da kulle jihar na tsawon mako biyu domin dakile yaduwar korona.