'Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Nijar

Aƙalla mutum 20 aka kashe a wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai a wasu ƙauyukan Nijar, a cewar hukumomin yankin.

Gwamnan Jihar Tillaberi, Tidjani Ibrahim Katiella, ya ce maharan sun shiga ƙauyukan a kan babura yayin harin na ranar Asabar.

Maharan waɗanda ba a san ko su wane ne ba, sun debe kayan shaguna sannan suka sace shanu tare da umartar mazauna kauyukan da su fice daga gidajensu.

Waɗanda suka shaida lamarin sun fada wa wata kafar yada labarai a Nijar cewa ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, inda suka hari garuruwan da suka haɗa da Gadabo da Koira da Teguio.

Jihar Tillaberi na cikin dokar ta-baci tun cikin shekarar 2017, wadda ke da iyaka da ƙasashen Mali da Burkina Faso da Benin.

Ƙasashen na ci gaba da fama da ayyukan masu dauke da makamai, yayin da dubbai daga cikinsu ke zirga-zirga tsakanin kasashen uku.

A ranar Lahadi ma an kashe dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a garin Kidal na ƙasar Mali.

Tuni dai rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Mali ta yi Alla-wadai da harin.