Rashin Tsaro: Daruruwan mazauna kauyukan Sokoto sun tsere Nijar

Asalin hoton, Tambuwal Facebook Page
Rahotanni daga jihar Sakkwato na nuna cewa daruruwan mazauna kauyuka ne suka tsallaka iyaka zuwa cikin Jamhuriyar Nijar domin fakewa bayan da 'yan fashin daji suka fatattake su daga matsugunansu.
Wani mai magana da yawun masu kaurar ya shaida wa BBC cewa yanzu 'yan fashin ne ke iko da kauyukan har tara da ke karamar Hukumar Sabon -Birni-Gobir.
Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin sun shiga kauyukan ne domin gujewa hare-haren da sojojin Najeriya ke kai musu ba kakkautawa a dajin Zurmi na jihar Zamfara mai makwabtaka.
Ga dai abin wani mai magana da yawun mazauna garin Dama da aka fattaka ya shaida wa Haruna Shehu Tangaza:
A makon da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya wani taro na musamman da masu ruwa da tsaki don tattaunawa kan here-hare a yankin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto.
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba ne ya bayyana wa BBC haka ranar Asabar.
A daren Juma'a 24 ga watan Afrilu zuwa wayewar garin ranar ne wasu 'yan bindiga suka kai hari wasu kauyuka a yankin Sabon Birnin Gobir da ke jihar ta Sokoto inda suka kashe akalla mutum biyu, sannan suka jikkata wasu da dama.
KArin labarai da za ku so ku karanta












