Coronavirus a Comoros: An harba hayaki mai sa hawaye cikin masallaci

Asalin hoton, AFP
Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa wasu mutane da suka taru a masallatai don gudanar da sallah, abin da ya saba wa ka'idojin kulle da hukumomi suka sanya a Komoros.
Gwamnatin Komoros ta sanya matakan ne don yaki da kwayar cutar korona wadda zuwa yanzu ba ta kai ga bulla a kasar ba.
'Yan adawa dai sun yi Allah wadai da wannan mataki na jami'an tsaro wanda ya faru da maryacen Asabar cikin tsibirin Anjouan
Shugaba Azali Assoumani ya kakaba dokar hana fita da daddare, duk da yake tsibirin na daya daga cikin kasashe guda biyu na nahiyar Afirka wadanda har yanzu ba a samu bullar kwayar cutar korona ba.
Wani shaida ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "mutane sun ji raunuka, akasari ma sai ta tagogi suka tsere, akwai ma mutum guda da ya karya kafa".
Ya kara da cewa "har zuwa safiya ma ana iya jin warin hayaki mai sa hawayen da jami'an tsaro suka harba a yanki."
Mafi yawan mazauna tsibiran Komoros - wanda rukuni ne na tsibirai a tekun Indiya, musulmai ne.
Kawancen 'yan adawa ya yi tir da wannan mataki, inda ya ce sojojin gwamnatin Assoumani sun yi "amfani da hayaki mai sa hawaye da alburusai a kan masu zanga-zangar lumana" da sunan yaki da bazuwar cutar korona.
Ko da yake, gwamnatin kasar ta musanta wannan zargi.
Watan azumin Ramadan, lokaci ne da al'ummar Musulmi kan kauracewa ci da sha da kuma jima'i daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana kuma akasari sukan taru lokacin bude baki su sha ruwa tare sannan su yi sallah.










