Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guba ta kashe gomman ''yan Boko Haram' a gidan yari
Rahotanni daga Jamhuriyar Chadi na cewa ayarin wasu mutane da ake tsare da su bisa zargin kasancewarsu 'yan Boko Haram ne su 44 sun mutu ga alama sanadiyyar guba.
Tsararrun sun mutu ne bayan kama su a wani artabun soji na baya-bayan nan a kasar Chadi.
Babban mai shigar da kara na kasar ya bayyana ta kafar talbijin ranar Asabar inda ya tabbatar da cewa an gano gawa 44 ta 'yan Boko Haram din a dakin da ake tsare da su ranar Alhamis.
Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna burbushin gubar mai kisa ce ta sanya zuciyar wasu daga cikin mutanen ta buga.
"Wasu kuma sun mutu sakamakon matsanancin rashin iska," in ji shi.
Sai dai bai ce komai game da wanda ke da alhakin mace-macen nasu ba.
A cikin watan Maris ne aka kama masu ikirarin jihadin a wani artabu da Shugaba Idris Derby ya ba da umarnin kai wa bayan kashe sojojin kasar kusan 100.
Mayakan Boko Haram sun kai harin ne kan wani sansanin soja inda suka haddasa wannan mummunar barna ga rundunar sojin kasar Chadi.
Ita ce asara mafi girma da aka taba yi wa sojojin Chadi a cikin rana guda, abin da ya harzuka Shugaba Derby har ya ce dakarunsa ba za su sake shiga duk wani shirin hadin gwiwar soja a wajen kasar ba.
Daga bisani dai ya sauya shawara bayan tuntuba a tsakanin kasashen yankin Tafkin Chadi, mai fama da ayyukan ta'addanci.
A farkon watan Afrilu ma, sai da rundunar sojin Chadi ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 1,000 a wani artabu da ta yi da mayakan kungiyar a yankin Tafkin Chadi.
Kakakin rundunar sojin Kanar Azem Agouna ya ce an kashe dakarun Chadi 52 yayin arangamar da aka shafe tsawon kwana shida ana yi a tsakaninsu.