Borussia Dortmund ta yi wa Sancho albishir

Borussia Dortmund za ta kara wa dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, albashin euro 4m idan ya ki karbar tayin komawa kungiyoyin da ke buga Gasar Premier. (Bild, via Mirror)
Newcastle tana son sayen dan wasan Barcelona da Chile Arturo Vidal. An ce dan wasan mai shekara 32 yana son komawa kungiyar idan ta maye gurbin kocinta Steve Bruce da Max Allegri. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan Spaniya Pablo Mari, mai shekara 26, yana son mayar da zaman aronsa a Arsenal zuwa na dindindin daga Flamengo a bazara. (Sky Sports)
Za a rage albashin dan wasan Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, zuwa tsakanin euro 35-40m bayan annobar coronavirus. (AS)
Arsenal da Everton na sha'awar sayen dan wasan Celtic dan kasar Faransa Odsonne Edouard, mai shekara 22. (Le10 Sport - in French)
Arsenal ta tuntubi Reims a kan yiwuwar dauko dan wasan Faransa Axel Disasi, mai shekara 22. (Goal)
Liverpool ta bayyana sha'awarta ta dauko dan wasan tsakiya na InterMilan da Croatia Marcelo Brozovic, mai shekara 27. (Libero, via Mirror)
Sai dai Liverpool ba ta tuntubi RB Leipzig ba a kan yiwuwar dauko dan wasan Jamus mai shekara 24, Timo Werner. (General Anzeiger - in German)
Barcelona tana son sayar da dan wasan Brazil Philippe Coutinho - wanda yanzu haka yake zaman aro a Bayern Munich - kuma tana fatan wata kungiya da ke buga Gasar Premier za ta sayi dan wasan mai shekara 27. (Goal)
Liverpool za ta rage farashin da ta sanya a kan dan wasan Switzerland Xherdan Shaqiri, mai shekara 28, saboda annobar coronavirus. (Football Insider)











