Messi ba zai koma Inter Milan ba, Leboeuf ya gargadi Lampard kan Coutinho

Dan wasan Barcelona da Argentina Lionel Messi, mai shekara 32, ya wallafa sako a shafukan sada zumunta inda ya musanta rahotannin da ke cewa zai koma Inter Milan. (Instagram)
Everton ta yi amannar cewa samun damar da dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, zai yi ta yin aiki a karkashin jagorancin koci Carlo Ancelotti za ta sa ya sanya hannu a kwantaragi da kungiyar a bazara. (Football Insider)
Tsohon dan wasan bayan Chelsea Frank Leboeuf ya gargadi kocin kungiyar Frank Lampard game da yunkurinsa na dauko dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, daga Barcelona. (ESPN)
A gefe daya, Roma ta bai wa dan wasan Chelsea Pedro, mai shekara 32, damar komawa kungiyar ta Serie A club, a yayin da kwangilarsa ke karewa a Stamford Bridge a bazara. (Mirror)
Barcelona na son karbo dan wasan Portugal Joao Cancelo, mai shekara 25, daga Manchester City a wata yarjejeniya da za ta kai ga mikawa City Nelson Semedo, mai shekara 26. (Telegraph, subscription required)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce yana shirya daukar matakai "biyu ko uku" idan aka soma musayar 'yan kwallon kafa a bazara. (Sky Sports)
Tsohon dan wasan Barcelona Rivaldo, mai shekara 47, ya ce dan wasan Paris St-Germain mai shekara 21 Kylian Mbappe zai koma Real Madrid a karshen kakar wasa ta bana. (Betfair)
Arsenal da Manchester United na fafatawa don dauko dan wasan Bayern Munich mai shekara 25 Corentin Tolisso. (Foot Mercato, in French)
Tsohon golan Nigeria Dosu Joseph ya ce Odion Ighalo, mai shekara 30, ya yi bajintar da za ta sa a ba shi kwangilar zaman dindindin a Manchester United inda yake zaman aro daga Shanghai Shenhua. (Goal.com)
Dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 21, yana son zama a Jamus domin ya koma Bayern Munich da zarar an bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa. (Sky Germany)











