Ganduje ya tube Kwamishinan da ya yi murnar rasuwar Abba Kyari

Asalin hoton, @malammuhammadgarb
Gwamnan Kano Umar Abdullahi Ganguje ya tube kwamishinansa na ayyuka Engr. Mu'azu Magaji bayan wasu kalamansa da suka nuna yana murnar rasuwar Abba Kyari.
A sakon da kwamishinan ya wallafa a Facebook, Injiniya Muazu, ya bayyana cewa "nasara, nasara. Najeriya ta tsira, Abba Kyari ya mutu a cikin annoba."
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
Wadannan kalamai sun janyo masa kakkausan suka daga mabiyansa a shafin Facebook, inda wasu suke cewa bai kamata mai mukami kamar sa ya yi kalamai irin wadannan ba.
Wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar ya ce an tube kwamishinan ne bayan kalaman nasa, wandanda ya ce bai kiyaye ba.
Sanarwar tube kwamishinan ta ce, "ya kamata a matsayinsa na kwamishina ya mutunta ofishinsa ta hanyar kaucewa aikata duk wani abin da zai ci mutuncin ofishin.
"Ayyukan ma'aikacin gwamnati, na kashin kansa ko akasin haka, zai dawo ne kan gwamnati, don haka gwamnatin Ganduje ba za ta yadda mutane da ke rike da mukami suna yin gaban kansu ko akasin haka," in ji sanarwar.
Injiniya Mu'azu ya mayar da martani a wani sakon da ya sake wallafa a shafin na Facebook bayan matakin da gwamnatin Kano ta dauka akansa, inda ya ce "ya shiga layin murabus."

Asalin hoton, Muaz Magaji Facebook
Malam Abba Kyari ya rasu ne ranar Juma'a bayan ya yi fama da cutar korona.
Labarai masu alaka











