Coronavirus: Aisha, Jonathan, Atiku, Ahmed Lawan sun yi ta'aziyyar Abba Kyari

Asalin hoton, Nigeria Pesidency
Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari tana cikin manyan 'yan Najeriya da suka yi alhinin rasuwar Abba Kyari Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaba Muhammadu Buhari.
Aisha Buhari ta jajantawa uwar gidan marigayi Abba Kyari da iyalansa kan babban rashin da suka yi.
A cikin sakon da ta wallafa a Twitter ta ce: "Ina jajantawa Kulu Abba Kyari da kuma dukkanin iyalan Abba Kyari kan rasuwar miji da kuma uba.
Ta kuma yi wa marigayin addu'a: "Allah Ya yafe masa kura-kuransa Ya kuma ba shi Al Jannah Firdaus Ya ba iyalinsa hakurin rashin da suka yi".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Manyan 'yan siyasa da jami'an gwamnati da dama a Najeriya sun bayyana alhininsu game da mutuwar Shugaban Ma'aikatan bayan ya rasu a daren ranar Juma'a sakamakon cutar korona.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya mika ta'aziyyar rasuwar Abba Kyari ga iyalansa da Shugaba Buhari da kuma sauran 'yan Najeriya.
Jonathan ya ce: "Allah ya saka shi a Aljannah Firdaus kuma ya bai wa iyalansa da abokansa hakurin rashinsa a wannan lokaci na alhini."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ya kadu da rasuwarsa tare da yi masa addu'ar "Allah Ya sa Aljnna ce makoma".
"Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un. Na kadu da rasuwar Shugaban Ma'aikata, Abba Kyari. Allah Ya bai wa iyalansa hakuri, Ya yafe masa sannan Ya saka shi a Aljanna Firdaus. Ameen," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Har wa yau, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan ya yi addu'ar "Allah Ya ji kan Abba Kyari, Ya yafe masa kura-kurensa.
Ahmed Lawan ya kara da cewa "Allah Ya sa Aljannatu Firdaus ce makomarsa," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Kazalika, Tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, shi ma ya bayyana alhinin rasuwar Abba Kyari, inda ya jajantawa Iyalan mamacin da kuma shugaba Buhari a sakon da ya wallafa a Twitter.
Har wa yau, shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari ya mika ta'aziyyarsa a shafinsa na Twitter, inda ya ce Abba Kyari "mutumin kirki ne kuma mai kaunar Najeriya".
"Allah Ya yi masa rahama", a cewar Mele Kyari.
A ranar 24 ga watan Maris ne aka tabbatar da cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriyar ya kamu da cutar korona bayan komawarsa kasar daga Jamus.
Labarin ya ja hankalin 'yan kasar sosai saboda girman mukaminsa.
Abba Kyari shi ne babban jami'in gwamnatin kasar na farko da ya harbu da covid-19.
A ranar 29 ga watan Maris ne Abba Kyari ya rubuta wata wasika, inda yake cewa ya tafi Legas domin ci gaba da jinya a kashin kansa don ya dauke wa gwamnati nauyin kula da shi.
Tuni maudu'in mai sunan Abba Kyari ya rika tashe a shafin Twitter, inda 'yan Najeriya ke ta jajantawa tare da bayyana ra'ayoyinsu kan mutuwar tasa.











