Coronavirus ta kama shugaban kwamitin da ke yaki da ita a Kano

Asalin hoton, Kano State
Shugaban kwamitin da ke yaki da cutar korona a Kano ya kamu da cutar kamar yadda ma'aikatar lafiyar jihar ta sanar.
A sanarwar wadda aka wallafa a shafin Twitter na ma'aiakatar, kwamishinan Lafiyar jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce sakamakon gwajin cutar korona da aka yi wa shugabannin kwamitin ya nuna uku daga cikinsu suna dauke da cutar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Kano dai a yanzu ita ce ta uku wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya, baya ga Legas da Abuja, kuma har ma ta yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Laraba.
A yanzu dai mutum 21 ne ke dauke da cutar a jihar kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta sanar a shafinta na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

A hirarsa da BBC kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al'ummar jihar.
Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa 'A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya', ko da yake daga bisani an amince a rka daukar mutum biyu.
Su ma motocin haya, an hana su daukar mutane fiye da kima.
Kazalika, a ranar da maraice dokar hana shiga da fita ta fara aiki a jihar, inda zuwa Juma'a da safe birnin ya zama fayau kowa yana cikin gida.
Sannan malaman jihar ma sun amince da matakin dakatar da Sallar Juma'a don hana yaduwar cutar.
Mutane sun yi ta rububin sayen kayan abinci a ranar Alhamis inda kasuwanni suka cika makil.
Da ma tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.













