Coronavirus: Gwamnan Bauchi Bala Kaura ya warke

Asalin hoton, Bala Kaura Twitter
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya warke daga coronavirus bayan da sakamakon gwajinsa a karo na biyu ya fito, bayan shafe fiye da mako biyu yana jinya.
Gwamna Bala Muhammad Kaura da kansa ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis da maraice.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A ranar 24 ga watan Maris ne wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun babban mai bai wa gwamnan shawara kan yada labarai Mukhtar M Gidado, ta tabbatar da cewa gwamnan ya kamu da cutar.
Kuma tun a wancan lokacin ya killace kansa tare da dakatar da ayyukansa.
A sakon Twitter din Gwamna Bala ya ce: ''Alhamdulillah. Yanzun nan na samu sako mai dadi. Gwajina na biyu na coronavirus ya nuna ba na warke.
''Na gode muku dukka da adduo'inku da goyon bayanku. Sannan na gode wa Allah - Mai Rahama Mai Jin Kai.''
Shi ma a nasa sakon na Twitter, shugaban ma'aikatan fadar Bauchin Ladan Salihu ya kambama gwamnan da cewa ''Ina alfahari da gwamnana wanda ya yi biyayya tare da yin imani da hakuri da halin da ya tsinci kansa.
''Lallai ya nuna jagoranci na gari wajen killace kansa ba tare da ya karya ka'idar hakan ba.''

Asalin hoton, Bauchi
Zuwa yanzu dai an samu mutum takwas da ke dauke da cutar a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriyar.











