Jerin ringingimu tsakanin hukumar tace fina-finan Kano da Kannywood

Ganduje da Naziru da oscar
Lokacin karatu: Minti 4

Matakin da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da ke Najeriya ta dauka na dakatar da nuna fitattun shirye-shiryen talbijin din nan masu suna 'Kwana Casa'in' da 'Gidan Badamasi' ya jawo mata yabo da caccaka.

Shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa fina-finan biyu sun ci karo da tsarin dokokin hukumar, inda ya ce a shirin Kwana Cas'in an nuna maza na cacumar wata yarinya.

A shirin Gidan Badamasi kuma ya ce an yi amfani da kalaman da ba su dace ba, wadanda dukkaninsu a cewar Afakallah sun saba wa sashe na 102 na dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai a 2001.

Shirin 'Kwana Casa'in' ya shafi siyasa da kuma bankwado yadda rashawa ta yi katutu a harkokin gwamnati, wani dalilin da wasu ke ganin shi ya sa gwamnatin Kano ta yi amfani da hukumar tace fina-finai aka dakatar da nuna shirin.

Ba wannan ne karon farko da hukumar ta shiga ce-ce-ku-ce da wasu 'yan fim ba, wadanda a cewar suke karya dokokinta, ko da yake galibi masu harkar fim da mutanen gari na ganin hukumar tana haikewa ne kan mutanen da ke da bambancin ra'ayin siyasa da gwamnatin Kano.

Amma shugaban hukumar, Alhaji Isma'ila ya sha musanta zargin.

Ga jerin wasu ringingimu da suka faru tsakanin hukumar da 'yan Kannywood:

Sanusi Oscar

A watan Agusta na 2019, Hukumar ta gurfanar da daraktan fina-finai Sanusi Oscar a gaban kotu saboda ya "saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai badala a ciki", kamar yadda shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakallahu ya shaida wa BBC.

Oscar ya musanta zargin kuma alkali Aminu Fagge na kotun majistire da ke Kano ya bayar da belinsa bisa sharuda biyu — wajibi ne mutum biyu su tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya zama dan uwansa na jini, tare da haramcin magana da kowacce irin kafar yada labarai

Batun ya ja hankalin fitattun 'yan fim, ciki har da tauraruwar fina-finan Kudancin Najeriya, Kate Henshaw, wacce a sakon da ta wallafa a Instagram ta caccaki hukumar tace fina-finan.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Naziru Sarkin Waka

NAZIRU SARKIN WAKA

Asalin hoton, Instagram/Naziru Sarkin Waka

A watan Satumba na 2019, rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta kama fitaccen mawakin nan Naziru M. Ahmed, wanda aka fi sani Naziru Sarkin Waka "saboda kalaman batanci" da ya yi a cikin wasu wakokinsa.

Hukumar tace fina-finan, wacce ta bayar da umarnin kama shi, ta kara da cewa ana tuhumar mawakin da gudanar da dakin yin waka, wato sutudiyo, a gidansa, zargin da Naziru M. Ahmed ya musanta.

Naziru shi ne Sarkin Wakar Sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje lamarin da ya kai ga raba shi da sarauta.

Shi ma kotun Majistare a birnin Kano ta bayar da belinsa da sharuda wadanda suka hada da bayar da kudi naira dubu 500, da mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye, da kuma gabatar da mutane uku da za su tsaya masa, wadanda dole su kasance ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune.

Sani Danja

Sani Danja

Asalin hoton, Facebook/Sani Danja

A watan Fabrairu fitaccen tauraron fina-finan Kannywood, Sani Danja, ya yi zargin cewa hukumar tace fina-finan jihar Kano ta rufe kamfanin daukar hotonsa saboda siyasa.

Sai dai hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda kamfanin bai cika sharudanta na yin rijista ba.

Adam A. Zango

Kazalika a watan na Fabrairu, hukumar tace fina-finan ta sha alwashin kama fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Adam A. Zango idan ya je jihar domin gudanar da waka ko fim ba tare da yin rijista ba.

A wancan lokacin, Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'.

Afakallah ya shaida wa BBC cewa ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa.

Da ma dai akwai jikakkiya tsakanin hukumar da tauraron tun bayan da ta hana shi gudanar da wasa tana mai cewa sai ya yi rijista idan yana so ya gudanar da wasan.

Adam A. Zango ya yi ikirarin cewa hukumar ta bullo da batun yi wa daidakun taurari rijista ne saboda ta musguna masa, ko da yake hukumar ta musanta zargin.

Bayanan sautiAbin da ya sa na yi rigista da hukumar fina-finan Kano

Sai kuma wata takaddama da ta kunno kai tsakanin shugaban hukumar tace fina-finan da kuma jarumin fina-finan Kannywood, Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu.

Takaddamar ta samo asali ne bayan da aka aike wa Baban Chinedu wata takarda a kan wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram yana zargin cewa gwamnatin Kano ta bai wa shugaban hukumar tace fina-finan N5m domin mika su ga iyalan marigayi Rabilu Musa Ibro.

Baban Chinedu dai makusancin Ibro ne, kuma ya ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta bai wa Isma'il Na'abba Afakallah kudin ne a matsayin gudunmuwar bikin 'yar gidan marigayi Ibro kusan shekaru biyu da suka wuce.

Sai dai lauyoyin Malam Afakalla sun bukaci Baban Chinedu ya janye kalaman da ya yi ko kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Har yanzu dai batun yana kotu.

Masana harkokin fina-finan Kannywood sun ce irin wadannan rigingimu za su ci gaba da yin mummunan tasiri kan masana'antar, ko da yake hukumar tace fina-finan ta ce matakan da take dauka za su kawo gagarumin ci gaba a Kannywood da kuma tsaftace masana'antar.