Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Facebook da Twitter sun cire sakonnin shugabannin wasu kasashe
Facebook ya cire wani bidiyo da shugaban Brazil, Jair Bolsonaro ya wallafa a shafinsa, wanda ke cewa hydroxychloroquine na maganin coronavirus.
Shugaba Bolsonaro ya sha yin watsi da cutar kuma ya bukaci 'yan kasarsa su yi fatali da shawarwarin da likitoci ke bayarwa kan barin tazara.
Wannan ya biyo bayan cire wani sako da Shugaban Venezuela, Shugaba Nicolas Maduro ya wallafa, wanda ke dauke da bayanin yadda mutum zai sha maganin cutar a gida ba tare da zuwa asibiti ba.
Duka shafukan biyu na sada zumunta ba su cika kutse kan sakonnin da shugabanni ke wallafawa ba, ko da kuwa a ce ba gaskiya ba ne.
Misali, Twitter ya ce "zai yi kuskure idan ya bai cire sakon ba" idan shugabannin kasashe suka karya dokoki.
Amma duka manyan shafukan sada zumunta na fuskantar matsin lamba kan yaki da labaran bogi da suka shafi annobar coronavirus.
Twitter ya yi bitar dokokinsa na yaki da labaran karya kan lafiya, da ya ci karo da dokokin lafiya na kasa da kasa.
Kuma Facebook ya dauki mataki kusan irin wannan wajen cire duk wani labari da ka iya jawo illa.
Sakonnin Shugaba Bolsonaro sun nuna shi yana magana da mutane a titunan Taguatinga.
Facebook ya ce ya cire bidiyon ne daga Facebook da Instagram, saboda ya kauce wa ka'idojinta, kamar yada kamfanin ya shaida wa BBC.
Bayanan da kamfanin ya fitar daga baya ga shafukan labarai na intanet na Buzzfeed da The Verge, sun nuna cewa an cire sakonnin ne saboda hydroxychlorine.
Hukumar lafiya ta Duniya ta ce yayin da hade-haden wasu magunguna na iya yin tasiri kan cutar, kawo yanzu babu wani tsayayyen magani da ke warkar da cutar.
Kuma har yanzu ba a tabbatar da sahihancin amfani da hydroxychloroquine da sinadarin chloroquine a matsayin maganin cutar ba.
Sai dai duk da rashin gwaje-gwaje, a yanzu, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka, FDA, ta amince a fara amfani da magungunan biyu, wadanda magungunan malaria ne, wajen bai wa masu fama da Covid-19 da ke kwance a asibiti.
FDA ta ce yiwuwar amfaninsu ta fi illolin da za su iya yi.
Amma Shugaban Amurka Donald Trump ya tallata amfani da hydroxychloroquine a matsayin maganin cutar a makon da ya wuce, kafin FDA ta sana
Kuma an goge wani sako da lauyansa kuma tsohon magajin garin New York Rudy Giuliani, ya wallafa da ke cewa magungunan na maganin cutar dari bisa dari.
Ya ambato wani mai goyon bayan Shugaba Trump, Charlie Kirk, wanda shi ma aka goge wasu sakonni da ya wallafa.
A Burtaniya, an kafa wani kwamiti a ofishin Firai Minista da zai yi aiki da shafukan sada zumunta wajen cire labaran karya da bayanan da ka iya jawo illar.
Karin labaran da za ku so ku karanta